Matatar mai ta Dangote ta sanar da fara dakon man fetur da dizal a fadin kasar daga ranar 15 ga Agusta, 2025.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, matatar ta bayyana cewa shirin zai hada da ‘yan kasuwa, masu gidajen mai, masana’antun, kamfanonin sadarwa, kamfanonin jiragen sama, da sauran manyan masu amfani da man a fadin kasar nan.
A wani bangare na dabarun kasuwanci, matatar Dangote za ta yi dakon man kyauta, domin kawar da tsadar sufuri da kuma inganta harkar kasuwancin matatar a duk fadin kasar.
Domin saukaka aikin, matatar ta sayo sabbin tankunan dakon man mai amfani da iskar Gas (CNG) 4,000, wadanda za su zama kashin bayan dakon kayan zuwa inda ake bukata.