Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote (DIL), Alhaji Aliko Dangote, ya ce masu juya harkokin mai a bayan fage wadanda suke shafuffu da mai (Kabal’) a bangaren harkokin mai da iskar gas a Nijeriya su na ci gaba da yakar nasarar da matatarsa ta samu.
Dangote ya shaida hakan ne a lokacin da ke ganawa da kungiyar masu zuba hannun jari a Legas a karshen mako.
- Rage Farashin Man Fetur Na Dangote Ya Sa Wasu Gidajen Mai Na Kullewa
- Gobara A Haramtacciyar Wurin Ajiye Man Fetur Ta Ci Rayukan Mutane 5 A Jihar Ribas
“Tsawon lokaci, wadanda suke kwanciya a kan makuden kudaden da gwamnati take fitarwa da sunan tallafi na shigo da mai zuwa Nijeriya su ne wadanda suke ta kokarin yin zagon kasa ga matatar mai ta dala biliyan 20 da ke Lekki a Jihar Legas.
“Wadannan gungun mutanen su ne suka dauki nauyin adawa da cire tallafin mai da gwamnatin Bola Tinubu ta yi kuma suke tsananin adawa da matatar mai da ke kawo sauki ga jama’a a cikin kasar nan,” ya shaida.
Duk da hakan, Dangote bai karaya baya, cikin kwarin gwiwa, ya ce yakin da ke tsakanin matatar da ke da karfin fitar da ganga 650,000 na mai kowace rana kuma take sarrafa sinadarin mai na sama da dala biliyan 20 za ta yi nasara a kan wadannan ‘Kabal’ din masu neman hana ruwa gudu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp