Matatar man Ɗangote ta rage farashin man fetur, daga Naira 950 zuwa Naira 890 kan kowace lita, wanda ya fara aiki daga ranar Asabar 1 ga Fabrairu, 2025.
Wannan sauyin na zuwa ne biyo bayan sauye-sauye da aka samu a kasuwar makamashi da iskar gas ta duniya da kuma kyakkyawan tsarin kasuwanci don tabbatar da gaskiya da adalci na matatar man Ɗangote don neman sauki da mafita a koda yaushe ga abokan huldarta.
- Rashin Tsaro A Nijeriya: Gazawar Masu Mulki Ce Da Cin Amanar Kasa
- An Kammala Aikin Tsugunar Da Mutane A Gundumar Tingri Ta Sin Bayan Bala’in Girgizar Kasa
Matatar mai ta Ɗangote ta yi imanin cewa, wannan ragi daga Naira 950 zuwa Naira 890 zai haifar da raguwar farashin man fetur a fadin kasar nan, wanda hakan zai haifar da faduwar farashin kayayyakin masarufi, da tsadar rayuwa baki daya, tare da yin tasiri mai inganci a sassa daban-daban na tattalin arzikin Nijeriya.
Bugu da kari, matatar man Ɗangote ta yi kira ga ‘yan kasuwa da su bata hadin kai wajen rage farashin man su don ganin al’ummar Nijeriya sun amfana da wannan sauyin da aka samu a kasuwa.
Wannan hadin gwiwar zai taimaka wajen fadada shirin farfado da tattalin arzikin kasa karkashin jagorancin mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya dukufa wajen ganin Nijeriya ta dogara da kanta wajen tace man fetur da kuma sanya kasar a matsayin babbar cibiyar fitar da mai.