Tsohon gwamanan Jihar Zamfara kuma Karamin Ministan Tsaro, Bello Muhammed Matawalle ya bayyana cewa, kofar Jam’iyyar APC abude take idan gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal na Jamiyyar PDP na bukatar shigowa Jamiyyar.
Ministan ya bayyana haka ne a Mahaifarsa Maradun a lokacin ziyar Sallah da magoya bayan Jam’iyyar APC na Kananan Hukumomi 14 suka kai masa a gidansa da ke Maradun cikin Jihar Zamfara.
Matawalle ya bayyana cewa, muna jin rade-radin cewa , gwamna Dauda zai dawo Jam’iyyar APC sakamakon Jam’iyyar su ta PDP na fama da matsalar rikice-rikice. Domin yanzu haka da Sallar nan daya daga cikin gwamnonin PDP ya dawo APC A Legas.
Don haka, Kofarmu a bude take ga gwamna Dauda Lawal, zuwansa APC dan bamu kyama, kowa da kowa namune Indai ya shigo wannnan Jam’iyyar mai albarka ta APC.














