Sabon sauyin manyan hafsoshin tsaro da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a makon da ya gabata ya sake haifar da tambayoyi daga al’umma da masana tsaro, shin sauyin zai kawo sabon canji a sha’anin tsaro ko kuwa kamar yadda aka saba ne kawai, sauya shugabanni ba tare da sauya tsari ba?
A wannan lokacin da Tinubu ya canza shugabannin hukumomin tsaro na kasa a daidai lokacin da kasar ke ci-gaba da fuskantar tabarbarewar sha’anin tsaro, kallo ya koma kan rawar da sababbin shugabannin za su taka.
Jama’a da dama na ganin sauya shugabannin hukumomin tsaron mataki ne da gwamnati ta dauka domin sake canza fasalin sha’anin tsaro wasu kuwa na ganin tsofaffin fuskoki ne kawai a sababbin kayan damara.
A yanzu haka dai al’umma sun sa ido sosai domin ganin ko sababbin hafsoshin za su iya kawo gagarumin canji a yaki da ta’addanci da satar mutane a yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
A sama da shekaru biyu da shugabannin rundunar tsaro suka kwashe a fagen yakii da matsalar tsaro, al’ummar kasa na ci- gaba da bayyana rashin gamsuwa da ake gudanar da salon yaki da ta’addanci musamman rashin ganin kwakkwaran sakamako a kasa.
Shugabannin Rundunar tsaro da Tinubu ya sallama sun hada da shugaban rundunar tsaro ta kasa Janar Christopher Musa da shugaban sojojin ruwa, Emmanuel Ikechukwu Ogalla da shugaban sojojin sama Hassan Abubakar.
Wadanda suka maye gurbin su da idanu ya koma kan hobbasar kwazon da za su nuna su ne shugaban rundunar tsaro Olufemi Oluyede, shugaban sojojin kasa Waidi Shaibu, shugaban sojojin ruwa Idi Abbas da shugaban sojojin sama S.K Aneke sai kuma shugaban rundunar leken asiri, EAP Undiendeye wanda ya ci-gaba da rike kujerar sa.
Yan Nijeriya sun jima suna kukan duk da kwarewa da gogewar jami’an sojojin Nijeriya da irin makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro a kowace shekara amma matsalar kullum gaba- gaba take kara yi.
Yankuna da dama a Nijeriya musamman a Arewa- Maso- Yamma, Arewa- Maso- Gabas da Arewa ta tsakiya sun zama lahira kusa a bisa ga yadda barayin daji ke garkuwa da mutane, kone garuruwa da yi wa jama’a kisan kare dangi.
Gagarumar matsalar wadda tuni ta zama tamkar ruwan dare a tsayin shekaru ta ci dimbin rayuka da dukiyoyin al’umma ba adadi ba tare da samun gagarumar nasarar dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma ba.
Masana tsaro sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan sauye- sauyen. Wasu na ganin cewa sabbin jini za su iya kawo canji, yayin da wasu suka yi gargadin cewa sauya shugabanni kadai ba zai wadatar ba idan ba a yi gyaran tsari ba.
 
			




 
							







