Gwamnan Jihar Katsina ya bayyana matsalar tsaro a matsayin babban dalilin da ya haifar da koma-baya a bangaren ayyukan ci gaba na gwamnonin Arewa maso Yamma.
Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya tabbatar da haka ne lokacin da ya amashi bakuncin kwamitin kula da aiwatarwa da sanya ido na ayyukan da aka aiwatar a jiha daga gwmamnatin tarayya.
- Kotu Ta Sake Aike Murja Da Wasu ‘Yan TikTok 3 Zuwa Gidan Yari
- Xi Jinping Ya Ba Da Umarni A Yi Namijin Kokarin Ceto Wadanda Suka Bace Sakamakon Rugujewar Mahakar Ma’adinin Kwal A Jihar Mongoliya Ta Gida
Ya ce gwamnatocin jihohin da ke wannan shiyya sun kashe makudan kudade wajen samar wa hukumomin tsaro da ‘yan bijilanti tallafi wadanda ke yaki da ‘yan bindiga.
Masari ya ce gwamnatinsa na da cikakken bayani dalla-dalla na dukkan ayyukan da ta yi da suka hada da ayyukan ci gaban gine-gine da na sha’anonin tsaro tun daga 2015 har zuwa yau.
Gwamnan ya kuma nuna jin dadi ga majalisar zartarwa ta kasa game da kafa kwamitin da zai zagaya jihohin kasar nan don auna ayyukan da kowane gwamna ya yi.
Ya yi fatan ganin cewa duk abin da kwamitin ya gano zai tabbatar da shi ga majalisar tattalin arziki ta kasa don daukar matakin da ya kamata.
A nashi bangaren, babban sakataren ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arizi, Alhaji Abdullahi Gagare ya ce ofishinsa ya gabatar wa kwamitin jerin ayyuka 28 manya-manya wadanda gwamnati mai ci yanzu ta aiwatar a shiyoyi na jihar, don kwamitin ya auna ya gani.
Alhaji Gagare ya ce tuni kwamitin ya ziyarci irin wadannan ayyuka da aka gudanar cikin babban birnin jihar.
Tun farko jagoran tawagar duba ayyukan, Mista Kanu N. Kanu ya ce kwamitin wanda aka dora wa alhakin karade shiyyar arewa maso yamman ya zo Jihar Katsina ne don duba ayyukan da gwamnatin jiha ta yi.
Ya ce kwamitin ya gamsu kuma ya samu natsuwa musamman yanayin kudin da aka kashe a kan kowane aiki cikin ayyukan da suka riga suka duba.