Ministan Wutar Lantar, Adedayo Adelabu, ya bayyana cewa, matsaloli ne da dama suka hadu suka dabaibaye shirin samar da ciakakken wutar lantar a fadin kasar nan. Ministan ya bayyana haka ne a martaninsa na cewa, bashi da cikakken kwarewa da masaniya a harkar wutar lantarki a kan haka ba zai iya magance matsalar da ake fuskanta ba.
Adelabu yana bayani ne a wani shiri na radiyo a garin Ibadan ta Jihar Oyo, wanda Wakilinmu ya nakalto mana, ya ce, matsalolin sun kasu kasha da dama da suka hada da na kayan aiki da kuma tsara tafiyar da aikin.
- Jamus Za Ta Zuba Jari A Harkar Noma, Kasuwanci Da Lantarki A Jihar Inugu
- Kar Turai Ta Yi Watsi Da Damar Daidaita Takaddamarta Da Sin Kan Motoci Masu Amfani Da Lantarki
Ya ce, Nijeriya na bukatar wanda zai magance matsalar da ake fuskanta ne ba wai dole sai injiniya ba.
“A gaskiya, matsalar mu a bangaren wutar lantarki ba wai maganar da ya shafi injiniyanci ba ne amma muna bukatar wanda zai shigo ne ya yi mana maganin matsalar da ta dame mu kawai ba sai injiniya ba,” in ji shi.
Ministan ya kuma ce, Shugaban Kasa Bola Tinubu bai nada shi don ya kera wayoyin wuta ko transfoma ba ne amma sai don yin nazarin halin da ake ciki tare da samar da hanyoyin maganinsiu.
Ya ce, da ya hau kan karagar mulki ya yi nazarin matsalolin da ake fuskanta, domin mutum ba zai iya maganin matsala ba har sai ya san nau’in matsalar, kuma dole ka gaya wa kan ka gaskiya ba tare da yaudara ba.
Ya kara da cewa, “Mun yi nazari tare da neman hadin kan masu ruwa da tsaki a bangaren samar da wutar lantarki inda muka fahimmaci matsalolin. Mun yi taruka da dama inda muka asamar da kundin da ke tattare da hanyoyin magance matsalolin da muka gano, a nan ne na nemi duk mu daina korafi mu fuskanci yadda za mu gyara abin da ke a gaban mu.”
Cikin hanyoyin da muke fatan magance wadannan matsalolin shi ne samar da dokar da zai kai ga ba kamfanomin masu zaman kansu su shigo domin su bayar da nasu gudummawar, kamar dai yadda shugaba Tinubu ya sanya wa dokar ‘Electricity Act 2023’ hannu a kwanakin baya