Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce matsayar kasar Sin a bayyane take, kuma ba ta sauya ba, dangane da batutuwan cinikayya dake tsakaninta da tsagin Amurka, kuma Sin ta yi amannar cewa, ba wani bangare da zai ci gajiya daga yakin haraji da na cinikayya.
Guo Jiakun, ya bayyana hakan ne a yau Litinin, yayin taron manema labarai na yau da kullum, lokacin da yake martani dangane da wasu rahotanni daga kafofin watsa labaran Amurka, dake cewa bangaren Amurkan ya lasafta ma’adanin farin karfe na “rare earths”, da sinadarin fentanyl, da waken soya, a matsayin manyan abubuwa uku da Amurka za ta dora muhimmanci kansu yayin tattaunawa da bangaren Sin.
Ya ce kamata ya yi sassan biyu su warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar shawarwari, bisa daidaito, da martaba juna da cimma moriya tare. (Saminu Alhassan)