Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta koka da cewa mafi akasarin gwamnoni sun yi watsi da jihohinsu, inda suka tare a Abuja, Babban Birnin Tarayyar kasar nan, yayin da kuma al’ummarsu da ya dace su na jagoranta su kuma suna can su na fama da matsin rayuwa.
Shugaban NLC na kasa, Mista Joe Ajaero, shi ne ya shaida hakan a yayin wata ganawa da ma’aikata wanda aka gudanar a sakatariyar NLC da ke Lokoja ta Jihar Kogi.
Shugabannin NLC sun kasance a Jihar Kogi ne domin kaddamar da fara amfani da motoci masu amfani da gas guda 10 da aka bai wa kungiyar reshen jihar domin saukaka lamuran sufuri.
- Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Nijeriya Da ‘Yan Kwadago Sun Tashi Taro Babu Matsaya
- Ɗalibin Jami’a Ya Hallaka Kansa Saboda Matsin Rayuwa A Jihar Kwara
Ajaero, ya ce sun ziyarci shiyyoyi guda biyar, kuma abun takaici duk sun tarar gwamnonin jihohin ba su nan, sun yi tafiya zuwa Abuja.
A daidai lokacin da ke tabbatar da matsin rayuwa da ake ciki da tabarbarewar tattalin arziki. Ajaero ya ce muddin gwamnatin ta ba da dama aka kara farashin cajin kamfanonin sadarwa, to lallai ma’aikata za su kara fadawa cikin matsatsin rayuwa.
Ya ce Jihar Kogi ce ta gudanar da taron domin tana da shugabannin kungiyar a matsayin gwamna da mataimakinsa, inda ya ce Gwamna Usman Ododo na daya daga cikin jami’ansa a Jihar Neja sannan kuma mataimakin jami’in kungiyar malamai ta Nijeriya (NUT).
Ya ce, “Don haka muna son mu yi wannan taron ne domin mu saurare ku don sanin abin da aka yi da abin da ba a yi yadda ya kamata ba, don haka mu dauka mu kai musu.
“A gare mu, kamar zuwan gida ne. Muna so mu zo mu yi hulda da su don gano ko suna yin abubuwan da muke sukar wasu.”
Kan haramta kungiyoyin kwadago a kwalejojin jihar da gwamnatin baya ta Yahaya Bello ta yi kuwa, shugaban NLC ya nuna damuwa da cewa gwamnati ba ta da ikon haramta kungiyoyin da suke karkashin jeri na musamman na majalisa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp