Wani matukin jirgin sama kirar Airbus 350 TK204, mallakin kamfanin jiragen sama na Turkish Airlines, ya mutu bayan da ya fadi ya na tsaka da tuƙi a sararin samaniya.
Lamarin da ya tilasta wa jirgin saukar gaggawa a birnin New York.
- Da Ɗumi-ɗumi: Kamfanin NNPCL Ya Ƙara Farashin Man Fetur Zuwa Naira 1,030 Kowace Lita A Abuja.
- Tallafin Ambaliya: Ɗan Majalisa Ya Buƙaci Gwamnatin Sakkwato Ta Bayyana Yadda Ta Kashe Biliyan Uku
Lamarin ya faru ne a yau Laraba, bayan da jirgin da ya taso daga Amurka a kan hanyarsa ta zuwa birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya.
Mai magana da yawun kamfanin jirgin saman Yahya Ustun, ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na X (Twitter).
Ya bayyana cewa jirgin saman ya tashi ne daga birnin Seattle, da ke gabar tekun yammacin Amurka.
A cewarsa, bayan rashin nasara a yunƙurin bayar da agajin gaggawa ga matukin jirgin, ma’aikatan jirgin saman suka yanke shawarar saukar gaggawa, a filin jirgin sama mafi kusa amma saukarsu rai ya yi halinsa.