A yau mun kawo muku hirar da muka yi da wata hazika, Malama data shahara wajen tarbiyartar tare da ba mata shawarar yadda za su yi zaman aurensu ba tare da wata matsala ba, wato Hajiya Fatima Lawan.
Ga dai yadda hirara ta kasance kamar yadda wakiliyarmu Basira Nakura ta nakalto mana.
- An Gurfanar Da Matashi A Kotu Sakamakon Lakadawa Dan Sanda Dukan Kawo Wuka
- Taron Jagororin JKS Ya Jaddada Aiwatar Da Shawarwari Da Tsare-tsaren Babban Taron Wakilan Jam’iyyar Karo Na 20 Cikin Hadin Kai
Da farko masu karatu za su so jin cikakken sunan ki da tarihinki a takaice
Sunana Fatima Lawan Alima”a rufa bi Tasallah Nabilusi Bako wancan sunan mahaifi nane wannan kuma sunan mijina nane saboda wasu suna tunanin sunan mahaifi nane a’a sunan mijina Nabilisi Bako mahaifina shi ne Muhammad Lawan Ali
Tarihin rayuwata ni na taso ‘yar gidan makaranta ce saboda haka nataso a matsakaici ‘yar rayuwa.
Na yi karatun firamare dana sakandire koda yake jarrabawar da muka dauka a iya kokarin da mukai basu bamu takarda ba sai suka daukemu makarantar muka zana jarrabawa daga nan sai na shiga makarantar Legal wacce take makaranta ce ta koyon addinin Musulunci. Wannan kenan, na yi Difloma na yi Adbas a bangaren Nizaniya ma’ana wato (Na zamani kenan)
Amma a bangaren na addinin musulunci wanda ya fara bani ilimi shine mahaifina daga nan sai aka samu makarantar Allo sai kuma muka shiga makarantar islamiyya ta Malam Shehu Alkali wadda dama daga ita ne muka shiga makarantar gaba da firamare inda daga ita ne naci makarantar W.A.T.C wacce a lokacin take a Sharada, To amma ban samu zuwa ba sai aka yi min aure, lokacin da aka zo neman auren ne Mahaifina ya yi kokarin nuna musu cewar shi ya so in yi karatu mai dan zurfi, to amma da yake Allah ya nufa da aka kaini gidana, kasan cewar gidan da aka kaini gidan makaranta ne bangaren gidan uwar mijina gidan Malam Abubakar Ramadan, gidan kuma mahaifinsa shi ne gidan Alhaji Bako Mai Turare
Saboda haka ya yi kokarin ɗorani akan wannan harka ta ilimin addinin Musulunci
To Daga nan kuma sai aka zo duba da cewar nataba koyarwa tun ina da shekara goma a makarantar islamiyyar mu
Duba da Nazarin da malaman mu sukai sukaga cewar zamu iya rike hakan, daga nan mahaifin mai gida suka yi kwamiti don ganin cewar ana samun raunin ilimin mata a Jihar Kaduna aka yi a lokacin da aka yi wata jarrabawa ta tafiya Hajji aka ce sai masu karatu ne za su tafi sai Kano mata suka dinga fadowa -dan haka sai iyayen mu mazanmu ko yayyensu zance suka kafa wani kwamiti sukaga ya kamata lallai a baiwa mata ilimin bangaren addinin Musulunci dan suma sudinga haye Tambayoyi kamar yadda Kaduna suke yi lokacin,
Don haka da aka kafa kwamnatin sai aka sa da mazanmu sai suka ga cewar yakamata a samu wadanda za su dinga yi, take Maigidana ya ce ya bada arona duba da ganin cewar na taba karantarwa a baya sai mahaifinsa ya ce to itama karatun nata kadanne amma zamu bayar da ita kafin a samu wasu to daga nan aka dore.
To sai mahaifin mijina ya soma bani karatu wanda a silar wannan muka soma bude makarantu na mata mun fara da ta kwamiti to daga karshe abin yanayi da kadan da kadan karshe ma abin ya dawo hannuna gaba daya.
To sai ya kasance muna ta bude rassa a takaice, hakika mun samu cigaba da taimako sosai musamman ta bangaren mahaifin Mai Gidana ya bani karfin gwiwa sosai kuma ya yi wa mijina jan kunnen da gargadin kada ya ce zai hanani matukar rayuwarsa don haka duk inda zan je in bude raeshe ko in bada gudunmawa Mai gidana baya hanani.
A haka muka samu karatuttukan da muka yi wanda har ta kai takawomu ga matsayin da muke kai wanda a’umma take gani.
Taya kike iya fuskantar matsalolin mata Duba yadda kike mu’amala da mata ma bammanta wannan za ta zo ta ce miki ga matsalar ta waccan ma tac e miki ga matsalarta, ga yawan mace-macen aure a kasar Hausa ko meye yake janyo haka?
To Gaskiya mace-macen aure ya kan faru ne ta Rashin Hakuri da Rashin Ma’auratan basa duba tsakanin ko wane bangaren mazan da matan basa duba da yadda yanayin rayuwar da ake ciki
Ita mace bata duba da yanayin cewar ya mijin yake gwagwarmayar samowa shi kuma ba zai yi hakuri da tsusasa mata idan babu da yadda za ta yi kokari ta yi musu dabara ba.
Mafiya yawa mata suna hakuri da mazaje, maza abu ya hade musu biyu ga ko karancin samun aiki ko karancin jari ko karancin samun ubangida to maimakon idan ya zo ya nemi hadin kan matarsa matukar matar ta samu tarbiyya mai hankali ce zaki ga ta yi kokari taga wane abune za ta bi wanda za ta fitar da mijinta daga wannan halin da yake ciki to sai kiga an kasa samun wannan sai shi ya dau zafin kai ita kuma tana ganin ta ci wuya don abinda ke hannun ta duk yabi ya kare to inba a yi sa’a ba ta wannan bangaren sai kiga an samu mutuwar aure ta hanyar tambayar sa abinda bashi dashi sai kiga nan da nan ya dau zafi sai ya yi sakin aure, domin shi sakin aure baya hannun mace, maza su ke sakin aure kuma basa duba da yadda Allah Ta’ala ya ce suyi rikon mataye cewa,”Fa’ansuku hunna bima’arufin Aufariƙuhunna bi maaruf’ Sadakallahul Azeem (ku rike matayenku da abin da shari’a ta gindaya muku), a’a su kuma basa duba da abin da shari’a ta ce.
To a ganki wane ne yafi laifi matan ne ko mazan?
To gaskiya ni nafi ganin laifin mazan domin igiyar auren a hannunsu take kuma an riga an san cewa ita mace dole ne sai an yi hakuri da ita, domin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya nuna mana cewar ita mace hakarkarice wanda yake a tankware a jikin mutum idan ka yi kokarin matseta ka ce zaka mikar da ita tofa sai dai ta karye amma in kayi hakuri zaka ji dadin a tankwaren ba’a samunta dari bisa dari haka Allah ya yi mu don ya baiwa mazaje kuuwarsu ‘Arrijali kauwamuna alal Nisa’ don Allah ya fito da wannan darajar tasu. To kinga ba za a ce laifin mace ne don an yi saki ba. Da ace ana bin dokokin da Allah ya shimfida da aure bai mutu ba domin yana da tsari sai anbi tsarin kayi fada sai kayi gargadi sai abin yaki ne to shi ne sai wani hukunci da za ka yi sai a dauko adalai bangare biyu a bauko a bangaren mata a dauko bangaren maza in dai sun nemi sulhu to Allah zai sanya gyara a tsakanin su amma ba a daukar wannan tsarin, sai kaga mutum ko dan yana da kudi ya riga ya gama rugurguza yarinyar don maman ya saki ya dukunkule sai kiga da ya hango wata tana yi masa yanga sai yaje ya dumbuzota ya zo ya ci mutuncin ta gida wannan abune da yake lalata tarbiya sai kiga yara ‘yan shaye shaye ga sunan da yawan su wadanda iyayen su basa a gida ne. Amma da mazan za su yi hakuri su ci gaba da tattalin ta gidan ana gyara mace ta dawo ta yi gargar amma sai kiga ya sa mata tsana da hantara wata ma kiga ta samu matsala hankalin ta ya gushe saboda bakan ta mata da musguna mata da ya keyi. Bayan da kadauketa mutum ka dauke ta mai daraja ce mai mutumci ce maimakon in zaka karo wata ita ka sanyaya mata rai a a sai kiga ya baza mata da yawa malam bahaushe yana sakin matar sane in yazo aukar wata shi ne ake samun wadannan matsalolin amma idan aka yi wani duba ga wasu matan su suke jawa kansu matsala sai kiga mace daga haihuwa daya ko biyu ta maida kanta kazama kucaka tasaki ko ina tana shara ta saki Mama kasa yana lilo to taya zaka gano darajar ta amma takame kanta ta gyalgyale kanta ta ware yara gefe lokacin dawo warka ta taho tana yi maka Oyoyo dole ne zaka dinga samun farin ciki wannan kadanne daga cikin matsalolin mutuwar aure.