Al’ummar jihar Kano sun roki gwamnatin jihar da ta gyara bututun ruwan sha na al’umma, gabanin bikin Babbar sallah domin kawo karshen wahalhalun da ake fama da su a yanzu da kuma dakile barkewar cututtuka.
Wasu gungun mazauna garin da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya zanta da su a birnin jihar a ranar Lahadi, sun ce, yanzun ya zama dole ne gwamnati ta kawo karshen wahalhalun da ake ciki kan kalubalen rashin ruwa a jihar ta hanyar gyara bututun ruwan sha na jama’a.
Daga cikin wadanda suka zanta da kamfanin akwai:
Sheikh Sani Imran wanda ya ce rashin samar da ruwan sha, ya jawo wa jama’ar jihar damuwa matuka.
Imran ya ce rashin samar da ruwan sha na jama’a ne ya sa masu hali ke ta hakar rijiyar burtsatse a gidajensu.
Malam Haruna Ahmad, mazaunin Darmanawa Quartres, ya tabbatar da ikirarin cewa an yi wa ‘yar makwabcinsa ‘yar shekara 15 fyade a lokacin da take kokarin diban ruwa a rijiyar burtsatse da dare sabida wahalar rashin ruwa da ake fama da ita.
“Kowa ya dogara da Dangaruwa ne don samun ruwa na rayuwar yau da kullum, muna siyan jarkar ruwa a kan Naira 80 zuwa N100 gwargwadon nisan gidanka” inji wasu mazauna cikin garin jihar.
Gwamna Abba Yusuf bayan hawansa karagar mulki ya ayyana dokar ta-baci kan samar da ruwan, inda ya umurci hukumar ruwa ta jihar da ta gabatar da bukatunta na maido da ruwan domin daukar matakin gaggawa.