Mutanen kauyukan da ke Mallamawa da Mazau a yankin Tsamaye/Mai Lalle a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto sun yi murna da farin ciki bayan sojojin hadin guiwa na ‘Operation FANSAN YAMMA (OPFY)’ sun yi nasarar kashe manyan shugabannin ‘yan bindiga uku a yankin.
A cewar jami’in watsa labarai na OPFY, Kyaftin David Adewusi, sojojin ya yin kai hari sun yi nasarar kashe Kachalla Nagomma da Gurmu da Ali Yar Daribiyar, sun kuma ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda uku da makamai da babura a hannun su.
Ya bayyana cewa ’yan ta’addar da mabiyansu sun shiga yankin ne don karɓar kuɗaɗen fansa da harajin da suka ƙaƙaba wa mazauna, kafin sojoji su tare su.
Kyaftin Adewusi, ya ce wannan nasara ta haifar da farin ciki da annashuwa a tsakanin mutanen Mai Lalle da Tsamaye da Rimaye da wasu ƙauyuka a Sabon Birni da Goronyo, waɗanda suka daɗe suna fama da hare-haren ‘yan bindigar da aka kashe.
Ya kara da cewa OPFY na ci gaba da jajircewa wajen dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma da wasu sassan Arewa ta Tsakiya.
Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa nasarar ayyukan tsaro a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp