Cibiyar Manyan Mutane (NSCC) ta hada hannu da ofishin Majalisar Dinkin Duniya da mai kula da ayyukan jin kai don shirya tattaunawar masu ruwa da tsaki ta kwana daya, kan bikin ranar tsofaffi ta duniya ta 2023 (UN IDOP).
Taron wanda aka gudanar a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja, don girmama ranar kasa da kasa ta bana ga tsofaffi mai taken: “cika alkawuran da aka yi ga ‘yancin dan Adam na duniya ga tsofaffi.”
- Jami’ar Chicago Ta Tabbatar Da Sahihancin Shaidar Karatun Tinubu
- Wuta Ta Yi Ajalin Mutum 18 A Wajen Satar Danyen Man Fetur
Taken wannan rana ya nuna yadda aka cika shekaru 75 tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wannan rana.
Mazaunin Majalisar Dinkin Duniya kuma mai kula da ayyukan jin kai a Nijeriya, Mista Mathias Schmale, a kan jawabinsa na maraba ya ce: “Abin farin ciki ne na yi muku maraba da zuwa wannan bikin yayin da muke bikin ranar tsofaffi ta Najeriya da kuma ranar tsofaffi ta duniya.
“Bikin na yau ya ba mu damar yin tunani a kai. Tasirin sanarwa kan hakkin dan Adam na duniya da kuma kare hakkin tsofaffi.
“Tsofaffin mutane na ci gaba da fuskantar cikas game da hakkin dan Adam. Tsufa yanayi ne mai sarkakiya kuma mai yanayi da zai shafi kowannemu”.
Taron ya jadadda aniyar sake tabbatar da ainihin manufar ayyana hakkin dan Adam na duniya: don kiyaye hakkin kowa, ba tare da la’akari da shekaru ba, ko matsayin mutum ba.
Wadannan hakkoki sun kunshi rayuwa, ‘yanci, tsaro, ‘yanci daga wariya, cin zarafi, tashin hankali, da azabtarwa, da samun damar samun ilimi, karfafa tattalin arziki, adalci da yanayin abokantaka game da shekaru.