A farkon shekarar nan ta 2025, hadin gwiwar kungiyar BRICS ya samu wani sabon tagomashi. Inda a ranar 1 ga watan Janairun nan, a hukumance aka ayyana kasashen Kazakhstan, da Malaysia, da Cuba, da Bolivia, da Uganda a matsayin kasashe abokan tafiyar BRICS, kana a ranar 6 ga watan aka amince da kasar Indonesia a matsayin cikakkiyar mambar kawance na BRICS, mai kasashen Brazil, da Rasha, da Indonisiya, da Sin da Afirka ta Kudu.
Sabbin kare-karen dai sun bude wani sabon babi na bunkasa hadin gwiwar BRICS, wanda zai haifar da moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa da masu saurin samun bunkasa. Ko shakka babu, fadadar hadin gwiwar BRICS zai samar da gudummawa ga dunkulewar tattalin arzikin duniya, da kyautata jagorancin sassan kasa da kasa, da zaman lafiya da ci gaban duniya.
- Tattalin Arziki: Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Iya Ci Gaba Da Taimakawa Gwamnatin Tinubu Ba – Sarki Sanusi II
- Hisbah Ta Yi Kakkausan Gargaɗi Tare Da Kira Ga Iyaye Kan Kula Da Yara Bayan Samun Gawar Wasu 4
Bana shekaru kusan 20 ke nan da kafuwar BRICS. Kuma a yau, kasashe mambobinta na da kusan rabin jimillar al’ummun duniya, da kaso sama da 30 bisa dari na daukacin GDPn duniya, suna kuma samar da gudummawar sama da kaso 50 bisa dari na tattalin arzikin duniya. Wanda hakan ke nuni ga yadda kungiyar ta zama wani ginshiki na daidaita harkokin kasa da kasa. Tabbas ci gaba da fadadar BRICS, alama ce mai nuni ga kyakkyawan tasirin hadin gwiwar da hadakar ke wanzarwa.
Gudummawar Sin ga hadin gwiwar BRICS
A matsayin kasa mai ingiza hadin gwiwar BRICS, har kullum kasar Sin na nacewa ga zurfafa matakan da za su kai ga bunkasa kungiyar, da yayata goyon baya, da farfadowar kasashe masu tasowa da masu saurin samun ci gaba. Mun ga yadda kasar Sin ta sanar da aniyarta, ta tsarin da zai sanya BRICS ta taka karin rawar gani a fannonin wanzar da zaman lafiya, da kirkire-kirkire, da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da tabbatar da adalci, da musayar kut da kut tsakanin al’ummun sassa daban daban na duniya, tare da kira ga kasashen BRICS da su yi hadin kai wajen tsare juna, da kafa tushen ci gaba mai inganci, da ingiza ci gaba mai dorewa, matakin da masharhanta da dama ke ganin ya kyautu ya zamo abun koyi ga sauran kasashen duniya masu fada a ji, da masu karfin tattalin arziki. (Saminu Alhassan)