Rikici ya sake ɓulla a gasar Firimiya ta Nijeriya (NPFL) bayan tashi daga wasan mako na 12 tsakanin Katsina United FC da Barau FC, inda wani ɗan wasa, Nana Abraham na Barau FC, ya samu mummunan rauni bayan harin da magoya bayan Katsina United suka kai masa. Lamarin ya faru ne bayan Barau FC ta farke wasa da ci 1-1, wanda hakan ya fusata wasu magoya bayan gida da ke cikin filin wasa na Muhammad Dikko, a cikin birnin Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa a minti na 70 na wasan, an dakatar da fafatawar bayan da aka kai wa Nana Abraham hari. Wani hoto da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna ɗan wasan cikin jini, yayin da abokan wasansa da jami’an tsaro ke ƙoƙarin ƙwantar da tarzomar. Duk da shigar jami’an tsaro don dawo da doka da oda, an ruwaito cewa har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto babu wata sanarwa daga Katsina United ko kuma hukumar gudanarwar NPFL.
- Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu
- Firimiyar Nijeriya: Barau FC Ta Samu Nasarar Farko A Tarihinta
Wannan tashin hankali ya zo ƙasa da wata guda bayan irin wannan lamari a Kano, lokacin da magoya bayan Kano Pillars suka mamaye filin wasa na Sani Abacha Stadium bayan Shooting Stars (3SC) ta Ibadan ta farke wasa a mintunan ƙarshe. Hakan ya jawo tashin hankali, inda jami’an tsaro suka yi amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa magoya bayan da suka kai farmaki ga alƙalai da ƴan wasa.
A martanin da ta mayar, Hukumar NPFL ta yi Allah wadai da irin waɗannan hare-hare da ke barazana ga tsaron ƴan wasa da martabar gasar.
Hukumar ta ƙaƙabawa Kano Pillars tarar Naira miliyan 9.5, tare da rage musu maki uku da ƙwallaye uku, da kuma rufe filin wasa na Sani Abacha. Masana harkokin ƙwallon ƙafa sun buƙaci a ƙara tsaurara hukunci kan masu laifi da kuma inganta tsaro a filayen wasa don hana sake faruwar irin wannan mummunan al’amari.














