“A baya mun kasance na farko a duniya ta fannin ci gaban manyan ababen more rayuwa, amma yanzu an jera mu a matsayi na 14”, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayyana damuwarsa game da yanayin da kasarsa ke ciki ta fannin ababen more rayuwa a yayin da yake rangadi a jihar Maine da ke arewa maso gabashin kasar a kwanan baya, inda ya kara da cewa, “ban manta ba, kasar Sin ta kasance a matsayi na 17 ko 16 a baya, amma ga shi ta zamanto na biyu yanzu. Me ya faru? Abin bai dace ba.”
A hakika, ba wannan ne karo na farko da shugaba Biden ya kwatanta kasarsa da kasar Sin ta fannin ababen more rayuwa ba. A jawabin da ya gabatar a jihar North Carolina a watan Afrilun bara, ya kuma kwatanta filayen jirgin sama na kasashen biyu, inda ya ce, “idan dai na rufe idonka a daddare, kuma na kai ka filin jirgi na O’Hare, sa’an nan na kai ka wani filin jirgi na kasar Sin…lallai ya yiwu za ka dauka filin jirgi na kasar Sin namu ne, sakamakon yadda ya kasance na zamani matuka.”
Abin da ya fada haka yake, kasancewar Amurka kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya, amma ababen more rayuwa na kasar sun tsufa har wasu sun lalace, wadanda ba su cancanci matsayin kasar ta fannin tattalin arziki ba. Idan ba a manta ba, a watan Faburairun wannan shekara, wani jirgin kasa da ke dauke da sinadarai masu guba ya kauce daga layin dogo a jihar Ohio ta kasar Amurka, lamarin da ya haifar da matsalar gurbacewar muhallin wurin. Abin bakin ciki shi ne, irin haduran ba su lissaftuwa a kasar ta Amurka. Alkaluman da hukumar kididdigar harkokin zirga-zirga ta kasar Amurka ta samar sun shaida cewa, daga shekarar 1990 zuwa ta 2021, gaba daya an samu hadura 54539 na kaucewar jiragen kasa daga layukan dogo, wato kimanin 1704 a kowace shekara.
Hakan ya sa wani mai bibbiyar shafukan yanar gizo ya saka wani hoto na kwatanta ababen more rayuwa na kasar Sin da Amurka, wanda ya kuma rubuta cewa, Amurka na zuba makudan kudade a fannin aikin soja a kowace shekara, a yayin da kuma kasar Sin ke zuba kudin a fannin gina ababen more rayuwa. Akwai kuma wani da ya rubuta cewa, “kasafin kudi a fannin aikin soja ya kai dalar Amurka biliyan 820, gwamnati ta kuma kebe wa yakin Ukraine dala biliyan 100, amma da an ce muna bukatar kudin gina ababen more rayuwa a gida, to, za ka ji ’yan siyasa sun ce daga ina za a samu kudin?”
A hakika, kalaman sun tona mana wani babban dalilin da ya sa ake samun koma bayan ababen more rayuwa a kasar Amurka, wato sabo da an zuba jari ga yaki a maimakon aikin gine-gine a cikin gida.
Kasancewar Amurka kasar da ke da tarihi na tsawon shekaru sama da 240 kawai, amma yake-yaken da ta tada ko kuma ta sa hannunta sun kai har sama da 200. Sanin kowa ne yake-yake na kashe makudan kudade, don haka, gwamnatin kasar Amurka ta zuba tarin kudi a yake-yake. Alkaluman da cibiyar SIPRI mai nazarin zaman lafiyar duniya da ke birnin Stockholm ta samar a watan Afrilun bana sun shaida cewa, kasar Amurka ce ta fi yawan zuba kudade ta fannin aikin soja a duniya, wadda a shekarar 2022 kadai, kudin da ta zuba a fannin ya kai dalar Amurka biliyan 877, wanda har ya dau kaso 39% na kudin soja da kasashen duniya suka zuba baki daya.
Kasar Sin a nata bangaren, tana ganin cewa, tabbatar da ci gaban kasa shi ne tushen daidaita dukkan matsalolin da ake fuskanta. Don haka ma, gwamnatin kasar ta dora matukar muhimmanci a kan gina ababen more rayuwa da saukaka fatara da ba da ilmi da kiwon lafiya da dai sauran muhimman fannonin da ke tabbatar da ci gaban kasa, tare kuma da cimma gaggaruman nasarori. Ban da raya kanta, kasar Sin ta kuma gabatar da shawarar raya kasashen duniya, inda ta yi kokarin aiwatar da hadin gwiwa da kasashen duniya, don fatan ganin tabbatar da ci gaban kasa da kasa, musamman ma kasashe masu tasowa. In mun dauki misali da Afirka, bisa tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da na shawarar “ziri daya da hanya daya”, kasashen Afirka sun gane ma idanunsu manyan sauye-sauyen da suka faru gare su ta fannin ababen more rayuwa. Kawo yanzu, layin dogo da aka gina a kasashen Afirka bisa hadin gwiwar sassan biyu ya wuce kilomita dubu 10, baya ga hanyoyin mota da tsayinsu ya kai kusan kilomita dubu 100 da kuma gadoji kusan 1000 da tashoshin jiragen ruwa kusan 100, wadanda suka haifar da alfanu ga al’ummar kasashen.
Shugaba Biden na damuwa da koma bayan ababen more rayuwa a kasarsa, amma me ya haifar da hakan? Ya kamata ya yi tunani a kai. (Lubabatu Lei)