An kammala taron koli na kungiyar kasashen kusu maso gabashin Asiya wato ASEAN karo na 44 da na 45 a kwanakin baya a birnin Vientiane, fadar mulkin kasar Laos. A yayin taron kolin, an gudanar da taron shugabannin kasar Sin da kasashen kungiyar ASEAN karo na 27, inda bangarorin biyu suka sanar da cewa, an gama shawarwari mai samfurin 3.0 kan yankin ciniki cikin ‘yanci na Sin da kungiyar ASEAN. Wannan muhimmin mataki ne kan inganta tsarin raya tattalin arzikin gabashin Asiya baki daya, kana ya shaida cewa, bangarorin biyu sun nuna goyon baya ga ra’ayin bangarori daban daban da yin ciniki cikin ‘yanci. Firaministan kasar Sin Li Qiang ya gabatar da shawarwari uku kan hadin gwiwar Sin da kungiyar ASEAN a gun taron, inda ya yi kira ga kafa tsarin yin mu’amala da juna, da fadada hadin gwiwar sabbin sana’o’i, da kuma zurfafa mu’amalar al’adu. Wannan ya shaida cewa, kasar Sin tana son zurfafa hadin gwiwa da sada zumunta a tsakaninta da kasashen dake yankin.
A halin yanzu, ana samun babban sauyi a yanayin kasa da kasa da yankuna, wasu kasashe sun gabatar da ra’ayoyin yanke hulda da nuna adawa da juna, kana ana samun ra’ayin ba da kariya ga cinikayya a sassan duniya. Bisa wannan yanayi, Sin da kasashen kungiyar ASEAN sun kara yin hadin gwiwa da juna, me ya sa hakan? Dalilin da ya sa hakan shi ne, bangarorin biyu suna da burin farfado da kasa da kyautata zaman rayuwar jama’arsu, kana a matsayin kasashen dake makwabtaka da juna, suna bukatar juna a fannin tattalin arziki, kana suna da damar samun bunkasuwa tare da moriyar juna.
Bisa sakamakon da aka samu a gun taron kolin kungiyar ASEAN a wannan karo, bangarori daban daban sun cimma daidaito kan goman yarjejeniyoyi, wannan ya shaida cewa, neman zaman lafiya da sa kaimi ga samun bunkasuwa su ne bukatun kasashen dake yankin, matakan tada rikici da zaune-tsaye ba su samu goyon baya ba. Ya kamata a bude kofa ga kasashen waje, da amincewa da bambance-bambance a tsakanin kasa da kasa, tsarin kungiyar NATO mai yada ra’ayin yakin cacar baka dake tsakanin kasashe masu tsarin jari-hujja da masu bin tsarin gurguzu da nuna adawa da juna a tsakanin kungiyoyi daban daban ba zai samu nasara ba. (Zainab Zhang)