Yanzu haka, an fitar da motoci kirar kasar Sin zuwa kasashe da yankuna fiye da 200. Alkaluman da kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin ta fitar jiya Alhamis, sun nuna cewa, yawan motocin da kasar Sin ta kera ta kuma sayar da su, ya zarce miliyan 30 a karon farko a shekarar 2023, wanda ya zama na daya a duniya a karo na 15 a jere. Abin lura shi ne, motocin da aka fitar zuwa kasashen waje sun kai miliyan 4.91, daga cikinsu miliyan 1.203 masu amfani da sabbin makamashi ne, wanda ya kai kashi daya bisa hudu na jimillar motocin da aka fitar.
Kafofin yada labaran kasar Japan sun bayyana cewa, hakan na nufin kasar Sin ta zarce kasar Japan inda ta zama kasar da ta fi fitar da motoci a duniya.
Me ya sa duniya ke son motoci kirar kasar Sin? A cewar kwararrun da abin ya shafa, wannan da farko yana da nasaba da samun ci gaba a fannin fasaha da ingancin motocin kasar Sin a shekarun baya-bayan nan, da karuwar karbuwarsu daga masu amfani da kayayyaki a duniya. Musamman ma, kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin sun yi amfani da damar da aka samu a cikin sabuwar kasuwar motoci masu amfani da sabbin makamashi ta hanyar fasahar kere-kere, da kara fadada kasuwannin ketare, da fitar da motoci zuwa kasashen waje. (Mai fassara: Ibrahim)