Birnin Taicang dake lardin Jiangsu na kasar Sin birni ne da ake kiran shi da sunan birnin kamfanonin kasar Jamus a kasar Sin, domin kamfanonin kasar Jamus fiye da 560 suna aiwatar da harkokinsu a wurin, ciki har da kamfanoni fiye da 60 da suka fi samun ci gaba a wasu kananan fannoni. Watakila wadannan kamfanoni ba su yi girma ko yin suna sosai ba, amma sun zama matsayin gaba a duniya a matakan wasu kananan fannoni, me ya sa Sin ta jawo hankalinsu sosai?
Shugaban reshen kamfanin Knorr-Bremse AG dake kasar Sin Bi Guanghong ya yi bayanin cewa, masana’antun kasar Sin sun zama matsayin farko a duniya, kana babu bukatar kashe kudi da yawa, da daidaita matsaloli cikin sauri, da kuma shafar fannoni mafi yawa. Idan aka gamu da matsala, gwamnatin kasar Sin za ta samar da taimako, wannan ne dalilin da ya sa aka raya wannan sha’ani mafi kyau.
Manajan reshen kamfanin Wessel Household Appliances na kasar Jamus dake kasar Sin Francis Kremer ya yi nuni da cewa, ana iya gama bincike da nazari a cikin makwani 4 ko 6 ko 8 a kasar Sin, lokacin ya fi sauri idan aka kwantanta shi da sauran kasashen duniya. Kana ana iya samar da kayayyaki a kasar kai tsaye, inda lamarin yake da muhimmanci sosai. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp