A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta tabbata cewa ta fadi daga gasar Firimiyar Nijeriya bana duk da nasarar da ta samu a wasanta na karshe akan Shooting Stars da ci 2-1 a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a nan Kano.
Wannan dai shi ne karo na uku da kungiyar ta fada ajin gajiyayyu a tarihi tun bayan kafa ta a shekarar 1990, Pillars dai ta taba faduwa daga gasar Firimiya a shekarar 1994 da 1999, sai kuma wannan karon.
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars dai ta taba lashe gasar firimiyar Nigeriya sau hudu inda ta lashe a shekarar 2008 da 2012 da 2013 sai kuma kakar wasa ta 2014, sannan a shekarar 2019 ta lashe gasar Aito Cup.
Kano Pillars tana da tarihi a fagen kwallon kafa a Nigeriya da kuma nahiyar Afirka, inda ko a shekarar 2009 sai da kungiyar ta samu damar zuwa wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Sai dai me ya sa Pillars din ta fada ajin gajiyayyu?
Rashin Kwararren Shugaba
Mutane da dama dai suna ganin shugaban kungiyar, Surajo Yahaya Jambul, wanda aka dakatar, bashi da cikakkiyar kwarewar da zai iya jan ragamar kungiyar hart a samu irin ci gaban da ake bukata musamman saboda rashin kwarewarsa akan harkokin wasanni.
A shekara ta 2019 ne gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada Surajo Shu’aibu Yahaya da ake kira Jambul a matsayin shugaban kungiyar ta Kano Pillars sai dai tun bayan da aka nada shi shugabanci wasu suka fara korafin cewar bai da kwarewar jan ragamar babbar kungiya kamar Pillars.
Magoya bayan kungiyar dai na ganin bai kamata tun farko a sauya tsohon shugaban kungiyar ba, Alhaji Tukur Babangida, wanda ya goge a sanin kwallon kafar kasar nan da kuma shige-shigen da ake yi a harkar.
Surajo Jambul ya karbi shugabancin kungiyar a lokacin da kungiyar take dab da daukar gasar cin kofin kalubale ta Aiteo Cup sannan kuma kungiyar ta yi ta biyu a kakar da aka kammala a lokacin.
Amma sai dai a kakar ya ja ragamar kungiyar ta yi ban kwana da gasar kofin Zakarun Afirka wato Champions League, inda Ashanti Kotoko ta Ghana ta yi nasara a kan Pillars 5-2 gida da waje sannan a kakar gaba aka yi waje da Pillars a gasar Confederation Cup, kuma wata karamar kungiya ta Senegal mai suna Jaraaf, wadda ta ci Pillars din 3-1 gida da waje.
Sannan bayan kasa taka rawar gani a wasannin zakarun Afirka, Kano Pillars ta ci gaba da rashin kokari a wasannin da take buga wa a Firimiya wanda magoya bayan kungiyar tun a wancan lokacin suka dinga kiraye-kiraye akan a kawo canji.
Bugu da kari, wasu suna ganin gwamnatin Jihar Kano ta janye daga bai wa Kano Pillars kudi kamar yadda aka saba yi, in banda albashin ‘yan wasa wanda hakan ya sa ‘yan wasa suka koma ba sa samun ladan wasa da sauran kudaden da suke kara karsashin ‘yan kwallo domin suke saka kwazo.
Amma wasu sun ce gwamnatin ko ta bayar da kudi kwalliya ba ta biyan kudin sabulu, saboda rashin kwarewar shugabanci wanda yana daya daga cikin abin da aka zargi kungiyar da shi tun farkon fara wannan kakar.
Rashin Buga Wasannin Gida A Kano
Kano Pillars ta koma buga wasanninta na gida a Jihar Kaduna, filin da ake kira Ahmadu Bello daga nan ta koma Jihar Katsina, filin wasa na Muhammadu Dikko sannan kuma daga nan ta koma wasa a Kano nan da nan kungiyar ta yi laifin da aka dauke ta zuwa Abuja, filin MKO Abiola na babban birnin tarayya, har ila yau daga nan kuma Pillars ta sake komawa buga wasanninta na gida a Sani Abacha da ke kofar mata, a Kano.
A dai kakar bana da Pillars ke fatan hada maki sai kungiyar ta ci karo da koma bayan da aka ci gaba da zargin Jambul da rashin iya gudanar da mulki sannan matsi ya ci gaba da hawan shugaban, wanda magoya baya suke ta shakkun da kyar idan kungiyar ba ta yi abin kunya ba.
Kwashe wa kungiyar Maki Shida
Tun bayan da Kano Pillars ta koma Kano buga wasa wato filin wasa na Sani Abacha, an samu yamutsin fasa motar Katsina United cikin watan Afirilu sannan an kara kwashe mata maki uku daga Kano Pillars kan laifin da Jambul ya aikata a karawa da kungiyar Dakkada.
Hukumar gudanar da gasar Firimiya ta kasa, LMC ta dakatar da shugaban Kano Pillars, Suraj Yahaya daga shiga harkokin wasanninta nan take bayan da aka tuhumi Kano Pillars da karya doka ta gudanar da wasannin Firimiya a lokacin da ta buga karawa da Dakkada ranar 23 ga watan Yunin 2022.
Halayyar magoya baya
Kungiyar magoya bayan Kano Pillars mai dunbin magoya baya itama ta bayar da gudunmawa wajen faduwar kungiyar daga gasar Firimiya a bana saboda yadda magoya bayan suka kasa nuna halin da’a a wasannin da ta buga a Kaduna da Katsina, wanda hukumar gudanar da gasar ta Nijeriya ke ta gargadinsu.
Maganar rikici da tayar da yamutsi ba abin da yake kawo ci gaba ba ne a kungiyar, amma magoya bayan Pillars sun yi suna a rashin hakuri a lokacin buga wasa kuma za’a iya cewa a yanzu wannan halayya ta jawo wa kungiyar koma baya.
Sannan ana ganin cewar Kano Pillars ba ta dauki ‘yan wasan da suka da ce ba musamman a kakar nan, idan ba haka ba ya kamata su fahimci cewar sana’arsu ce ba wanda zai kama musu sai dai kwazonsu.
Amma kuma rashin samun kudi a kan kari ya taka rawar gani da ‘yan kwallon suka kasa sa kwazo a wasanninsu, ga tarin matsaloli sannan bayan da abubuwa suka yi lalacewar da ba damar gyara, shi ne aka kori Surajo Shu’aibu Yahaya aka nada Alhaji Ibrahim Galadima na rikon kwarya.
Kungiyar Kano Pillars ta karkare a mataki na 19 da maki 45, bayan da ta ci wasa tara da canjaras tara aka doke ta karawa 20.
Haka kuma an zura kwallo 50 a ragar Pillars, ita kuma ta ci 26 a kakar bana da hakan ya sa ta yi ban kwana da babbar gasar ta Nijeriya da aka karkare amma sai dai kuma wasu na cewar watakila Kano Pillars ta buga gasar nan gaba, bayan da kungiyar Gombe mai suna Doma United ta samu gurbin shiga gasar kaka mai zuwa, amma wasu na cewar za ta sayar da gurbin ne.
An ce kungiyar ta Gombe na neman Naira miliyan 250 daga Kano Pillars, sai su yi musaya, masu gida ta koma Firimiya ita kuwa Doma ta ci gaba da buga rukuni na biyu kuma ba wannan karon bane ake cinikin gurbi a gasar firimiyar ta Nijeriya, domin Kwara United ta yi haka a shekarar 2019, haka itama Delta ta sayi gurbi a wajen Kada City.
Saboda haka wasu na ganin ya kamata a kawo sayen gurbi tsakanin kungiyoyi idan har ana son gasar ta yi armashi kuma yakamata a kafa dokar da za ta samar da fitattun kungiyoyin da za su ke wakiltar kasar a wasannin waje domin kai wa gurbin da ya kamata.