…Cigaba daga makon da ya gabata:
Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ko Kin San.
A yau shafin namu zai ci gaba da bayani kan farin ruwa na bayan ko kafin al’adar mace.
Wadannan ‘Hormones’ kamar su “progesterone” “oestrogen” “androgen” etc sauyin yanayinsu a jikinta ne ke sawa ta yi ta ganin “Al’aural discharge” yana fito mata.
Idan wani abu da ake kira da Turanci “estrogen” ne suka yi yawa a jikinta a lokacin, sai ruwan ya kasance fari-fari mai yauki kuma ruwa-ruwa.
Idan kuma “progesterone” ne suka yi yawa ajikinta, sai ruwan ya kasance farar madara kuma mai kauri-kauri.
Sannan ya launin ruwan yake kasancewa?
fari ne, ruwa-ruwa, madara-madara ne, yana da kauri ko akasin haka, muddin ba ya wari ko karni, gaban mace ba ya zafi, ka-kayi ko radadi, to wannan lafiya ne bashi da wata matsala.
Aikinsa (ruwan) shi ne, ya koro duk wani dattin Al’aura, wasu ‘Harmful germs’, da kuma ya sa Al’aura ta zama mai maski a kowane lokaci. Hakan yana nuna alamar duk wani abu na gaban mace yana da kyau ko kuma yana da lafiya sosai babu wata matsala a tattare da wajen.
Wasu lukota ne za ki yi tsammanin ganin farin ruwa a gabanki, Idan kin gani ba damuwa bane.
Yawancin mata suna iya samun bushewar gaba kamar na kwana 3 zuwa 4 kowanne bayan yankewar al’adarsu. Bayan wannan kwanakin, farin ruwa mai danko ya kan sake bullowa wanda zai yi kamar kwana 4 zuwa 5 kafin obulation, alama ce ta kwai su sun fara girma, ana kiran shi da “follicular phase” that means a lokacin ne “kwain” (for ovulation) suke kokarin girma.
Za mu ci gaba mako mai zuwa in sha Allah