Bikin baje kolin zuba jari da cinikayya na kasa da kasa na kasar Sin ko CIFIT a takaice da aka gudanar daga ranar 8 zuwa ta 11 ga wata, shi ne baje kolin kasa da kasa na farko dake da jigon zuba jari, wanda kasar Sin ta gudanar bayan kammala cikakken zama na uku na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar karo na 20. Haka kuma, ya kasance wata muhimmiyar taga ga masu zuba jari na kasashen waje ta fahimtar kasar Sin da neman damammaki a kasar. Wakilan kamfanoni na kasa da kasa da yawa sun bayyana cewa, ba za a wuce kasuwar kasar Sin ba, hakan ya sa “zuba jari a kasar Sin” ya zama kalmar da aka fi ambata a bikin.
Bisa sha’awar zuba jari, yawan sabbin kamfanonin da aka kafa da jarin waje a kasar Sin ya karu da kashi 11.4% daga watan Janairu zuwa Yulin bana. Daga mahangar aikin kasuwanci, jimilar ribar da kamfanoni da masana’antu masu jarin waje ke samu ta karu da kashi 11% a farkon rabin wannan shekara. “Rahoton zuba jari tsakanin kasar Sin da kasashen waje na shekarar 2024” da aka fitar a wani taron dandalin tattaunawa da aka yi yayin bikin CIFIT, ya nuna cewa, a shekarar 2023, kasar Sin ta ci gaba da kiyaye matsayinta na kasa ta biyu mafi jawo jarin waje a duniya, hakan ya sa ta ci gaba da kasancewa wurin da ake sha’awar zuba jari a duniya.
A yanzu haka ’yan kasuwar kasashen waje na kara zuba jari a kasar Sin ta hanyoyi daban-daban, kuma kasa da kasa na cin gajiya daga ci gaban kasar ta Sin. (Bilkisu Xin)