Masana harkar kwallon kafa sun bayyana cewar da wuya Brighton ta iya taka rawar gani kwatankwacin wanda ta yi a kakar da ta gabata. Shekarar da ta gabata kungiyar kwallon kafa ta Brighton And Hobe Albion, ta nuna wa duniya cewar ita ba kanwar lasa bace a harkar kwallon kafa inda ta dinga lallasa wasu daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa dake buga gasar Firimiya da suka hada da Manchester United da kuma Chelsea.
Ta ci gaba da taka rawar gani da har ya sa ta samu gurbin buga gasar Uefa Europa League a karon farko a tarihinta bayan ta kammala kakar bara a mataki na 6.
- Manchester United Zata Sayar Da Kashi 25 Na Kungiyar Akan Yuro Biliyan 1.3
- Newcastle Ta Dauki Harvey Barnes Daga Leicester City
Amma kamar zancen ya canza a bana domin kuwa a daidai wannan lokacin a bara Brighton tana mataki na uku, ba kamar bana da take ta 6 a teburin Firimiya ba bayan wasanni 8. Sannan kuma a gasar UEFA Europa League, Brighton tana zaune a karshen rukunin B bayan rashin nasara daya da canjaras daya.
Ba abin mamaki bane ganin cewar Brighton ta rabu da manyan ‘yan was anta da suka hada da Moses Caicedo da Mac Allister a kan kudade masu dimbin yawa. Wanda masu sharhi kan harkokin wasan kwallon kafa ke gani a matsayin wani babban dalilin da zai iya hana kungiyar tabuka wani abin a zo a gani a bana.
Kocin kungiyar De Zerbi yayin wata hira da ya yi da yan jarida ya bayyana cewar yana da matukar kwarin gwiwa akan ‘yan wasansa, kuma yana da yakinin cewar za su iya kai kungiyar inda ake da bukata.
De Zerbi ya karbi aikin horar da Brighton a bara bayan tashin tsohon kocinsu Graham Potter wanda ya koma Chelsea a kakar bara. Tun daga lokaci De Zerbi ya nuna kwarewarsa a harkar horarwa bayan jagorantar Brighton zuwa buga gasar UEFA Europa League.