Shafin Taskira shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa dabab-daban wadanda suka shafi al’umma.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin halin da kasa ke ciki wanda dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko ta wacce hanya ake ganin za a kawo zaman lafiya da ci gaban al’umma?”
- Zama Da Matsololin Miji Ga Matar Da Take Sana’a
- Yadda Bukukuwan Sallah Suka Kasance A Garuruwanmu – Mabiya Taskira
Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Hafsat Sa’eed, Daga Jihar Naija:
Hanyar da ya kamata abi wajen samun zaman lafiya ba wata hanya ba ce face a ce gwamnati ce ta tsaya a kai, saboda idan gwamnati ta so a yi zaman lafiya za a yi idan ba ta so ba ma haka dai, dan haka nake ganin gwamnati ita za ta kawo zaman lafiya a duniya da Najeriya. Shawarar da zan ba mu duka gabadaya da matasan mu masu tasowa shi ne; a tsaya a nemi na kai a nemi halak a guji sa’ido a kan abubuwan mutane rashin ji wani shaye-shaye wani iskanci, wani waye-waye duk a daina, a tsaya a jajirce a nemi ilimi me amfani ko dan makoma ranar gobe kiya.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya adalci ga shugabanin da kuma biyayya ta mabiya ita ce jigo na cigaban al’umma gabadaya ba wai matasa kadai ba, don haka muddun aka samu wadannan matakai a cikin al’umma to cigaba mai yawa zai wanzu a cikin al’umma. Neman ilimi ma yana daya daga cikin mataki na cigaban al’umma muddun matasa suka dage da neman ilimi to, za ka ga sun samar da cigaban mai dorewa a cikin al’ummar su.
Zaman lafiya ma yana daga cikin jigo dake samar da cigaban matasa domin babu wani abu dake gudana daidai sai da zaman lafiya. To, shawara a nan ita ce da farko ya kamata matasa su dage da neman ilimi domin shi ne fitilar rayuwa, domin sai da ilimi ne mutum zai san kansa, kuma ya kamata su yi kokarin kaucewa duk wani hali ko yanayi da zai jefa su harkar shaye-shaye domin yana daya daga cikin matsalolin dake addabar matasa a yau wanda kokarin magance ta zai kawo gagarimin cigaba a tsakanin matasa dama kasa bakidaya. Sai kuma shawara ta karshe iyaye ya kamata su tashi tsaye su kula da tarbiyya, yara tun suna kanana domin hakan zai taimaka wajen samun matasa nagari.
Sunana Khadija Shaaban Muhammad Kano State:
Ni a ganina hanyar da za a bi a kawo zaman lafiya da ci gaban al’umma, shi ne; a ba wa matasanmu aikin yi, sannan ‘yan kasuwa su yi hakuri su rage kudin kayan abinci, domin wasu su suke kara kudaden kayansu musamman masu ajiyewa a ‘store’ sai ki ga kayan shekara hudu an ajiye shi, ana jiran yayi tsada a fito da shi. ;Ya kamata matasanmu su farga su daina zaman banza, sana’a ko ya ya take ku yi ta, idan Allah ya taimakeku sai ku ga kun zama abin kwatance.
Sunana Aisha T. Bello Daga Jihar Kaduna:
Hanyar da za a kawo zaman lafiya da ci gaban al’umma ita ce: na farko a inganta tsaro yadda kowa zai samu kwanciyar hankali. Gwamnati tayi kokarin ganin kayan abinci da sauran kayan masarufi sun sauka yadda bai fi karfin talakka ba. Yunwa ba abin da ba ta sawa a rayuwa. A tabbatar ilimi bai gagari ‘ ya’yan talakkawa ba, domin jahilci shi ma ba abin da bai haddasawa. Shawarata ga matasa da sauran al’umma ita ce mu koma ga Allah, mu rungumi add’ua ita ce maganin komai a rayuwa, shuwagabanni su tausaya ma al’umma su tuna mutane suka yi fadi tashin zabar su a kan kujerar da suke, haka talakkawa mu duba cancanta ba wai a ba mu taliya ayi mana cutar shekara da shekaru ba. Matasa mu rika neman shawarar iyaye.
A kama sana’a ko da kana da degree ba aikin yi, a koyi sana’ar hannu mu rike kan mu, iyaye har ma da masu bukatar taimako, mu guji zaman banza wanda ke haddasa mutuwar zuciya wasu su shiga bara da kuma karfin su. Matasa a guji shaye-shaye don shi ne mabudin dukkan sharri, ya Allah ka kawo mana dauki da sauki a Najeriya.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, Daga Jos a Jihar Filato:
Fahimtar juna ce ke kawo zaman lafiya.
Zaman lafiya muhimmin al’amari ne ga cigaban kowacce al’umma. Sai da zaman lafiya ne ake samun kwanciyar hankali da natsuwar gudanar da duk wata hidima ta walwala da inganta rayuwa. Kamar su shiga siyasa da auratayya da wasanni, wadanda duk sai da zaman lafiya ake samun damar aiwatar da su. Gwamnati da mukarrabanta ba za su samu damar yi wa jama’a aiki ba, kuma hakan yana ba su damar warwason dukiyar jama’a da sunan gudanar da aikin da ayyukan tsaro.
Yana da muhimmanci jama’a su fahimci wannan, don su hada kai, kuma su samar da muhallin da za su fahimci bambance-bambancen da ke tsakaninsu, wanda shi ne ginshikin samun zaman lafiya. Shawarata ga matasa shi ne su sani fa shiga ayyukan tarzoma da tashin hankali, ko daukar doka a hannu, bai kamata da su ba. Don yana lalata cigaban kasarsu, jiharsu da garuruwansu. Yana kawo koma-baya da rashin walwala da rashin yarda da juna.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Rano LGA, Jihar Kano:
Addu’a da samarwa matasa ayyukan yi a kawar da son zuciya, a cire kabilanci da bambancin jam’iyya duba da yanzu komai ya koma hannun ‘yan siyasa. Shawarata ga matasa dama al umma bakidaya ita ce mu rike addu’a mu mikawa Allah komai namu, sannan muna duba suwaye shuwagabannin da za mu zaba sannan masu sana’a su rike ta mu daina raina sana’a komai kankantarta mu cire son zuciya, su kuma shuwagabanni suna tuna cewa kowa zai mutu har da su, sannan bayan mun mutu akwai wata rayuwar bayan mutuwa sannan za a yi wa kowa hisabi a kan dukkan abin da kowa ya aikata su rike amanar da rabbana ya basu. Allah kasa mudace amin.