Kwanan baya, wasu kafofin wata labaran kasashen yammacin duniya, da hukumar leken asiri ta kasar Amurka sun sake yada jita-jitar “Barazanar ‘yan leken asirin kasar Sin”, inda suka ce wai, ‘yan leken asirin kasar Sin sun saci sirri daga layoyin sadarwa da yanar gizo na kasar Amurka, don neman bata yanayin fahimtar juna dake tsakanin ‘yan siyasan kasashen Sin da Amurka, da kuma karfafa ra’ayi daya da bangarorin da abin ya shafa suka cimma wajen adawa da kasar Sin. A sa’i daya kuma, Amurka tana son karfafa aniyar sabuwar gwamnati a za a kafa a kasar, ta yin adawa da kasar Sin.
A hakika dai, kowa ya san wace kasa take gudanar da aikace-aikacen leken asiri. A shekarar 2013, tsohon ma’aikacin hukumar leken asiri ta kasar Amurka Edward Snowden ya bayyana sirrin tsarin PRISM na kasar Amurka, ya ce, kasar Amurka tana neman sa ido kan dukkan fannoni na yankunan yanar gizo na kasashen duniya. A ciki kuma, ta fi mai da hankali wajen sa ido kan harkokin kasar Sin. A hakika ta wadannan matakan da kasar Amurka ta dauka, ba zai yiwu ba ta boye burinta na cin zarafin kasar Sin, maimakon haka za ta kara bata sunanta da kanta. (Mai Fassara: Maryam Yang)