Hukumar ladabtarwar gasar MLS a Amurka ta ci tarar dan wasan gaba na Inter Miami Lionel Messi bayan samunsa da laifin yunkurin shako wuyan mai horar da kungiyar kwallon kafa ta New York City FC Mehdi Ballouchy a karawar da suka yi canjaras makon jiya.
Hukumar ta ce Messi mai shekaru 37 ya karya dokokin ladabtarwa na gasar MLS, dokokin da suka haramta yunkurin duka, ko kuma cutarwa kan duk wani abokin karawa ko mai horarwa a kowanne irin yanayi, Messi ya nufi mataimakin mai horar da kungiyar ta New York City FC wato Mehdi Ballouchy tare da saka hannunshi a wuyanshi a wani yanayi da ake kallo a matsayin rikici.
- Gwamnatin Kano Ta Amince Juma’a 28 Ga Fabrairu A Matsayin Ranar Hutun Zangon Karatu Na Biyu
- Matar Gwamnan Kebbi Ta Rarba Tallafin Kayan Noma Ga Mata Manoma 100
Duk da cewa ba a bayyana adadin kudin da aka ci tarar tauraron na Argentina ba, amma jaridun Amurka sun ruwaito mahukuntan gasar na cewa babu gurbin rashin da’a a MLS, wasan na ranar 22 ga watan Fabarairun ya tashi kunnen doki inda aka tashi da ci 2-2 tsakanin manyan kungiyoyin biyu dake buga babbar gasar MLS ta kasar Amurka.
Baya ga Messi shi ma Luis Suarez ya fuskanci hukunci bayan tuhumarsa da laifin dukan Birk Risa a wuya duk dai a wannan karawar tsakaninsu da New York, Messi ya koma Inter Miami daga PSG shekaru biyu da su ka gabata, tun bayan zuwanshi Miami Messi ya zura kwallaye fiye da 20 sannan ya taimaka an zura kwallaye da dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp