Uwargidan zababben shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, a ranar Laraba, ta bayyana cewa, mijinta zai tabbatar da cewa dukkan ‘yan gudun hijira a Nijeriya sun koma gida kuma sun cigaba da rayuwarsu ta yau da kullum.
Ta bayyana hakan ne a lokacin da take raba kayan abinci ga ‘yan gudun hijira a sansanonin Kuchingoro, Karamajiji da Gongola a babban birnin tarayya Abuja a wani bangare na shirin bikin rantsar da zababben shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.
Oluremi, wacce shugabar mata ta jam’iyyar APC, Dakta Betta Edu ta wakilta a wajen rabon kayan, ta bayar da tabbacin cewa mayar da ‘yan gudun hijirar gidajensu na daga cikin ajandar maigidanta (Tinubu).
“Matar zababben shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bukaci, mu je duk sansanonin ’yan gudun hijirar da ke kewayen Abuja da sauran gidajen hukumar NAPTIP, mu ba su wasu kayayyakin tallafi da za su taimaka wajen faranta wa ‘yan gudun hijiran a wani bangare na taya murnar shirin rantsar da maigidanta a matsayin sabon shugaban kasa a Nijeriya.” Inji shugabar Matan APC.