Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya ce karamin ministan gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata ba dan jam’iyyar ba ne.
Abdullahi Abbas ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan sakin baki da Yusuf Abdullahi Ata ya yi masa a kwanan baya yayin wata hira da BBC Hausa.
- NNPP Ta Dakatar da ‘Yan Majalisa Huɗu Bisa Zargin Yi Wa Jam’iyya Zagon Ƙasa
- Gwamnatin Katsina Ta Kashe Naira Biliyan 5.7 Wajen Sayen Awaki 40,000 Domin Raba Wa Mata
In ba a manta ba, ministan ya yi gargadin cewa, shi da magoya bayansa za su fice daga jam’iyyar APC idan aka mayar da Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar.
Ministan ya yi zargin cewa, furucin Shugaban na daya daga cikin dalilan da suka sa Allah ya karbe mulki daga jam’iyyar duk da nasarar da ta samu a zaben gwamna na 2023.
Amma da yake mayar da martani, Abbas ya yi zargin cewa Ata ya yi wa jam’iyyar zagon kasa a zaben 2023, kuma sun bayyana haka ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Abdullahi Abbas ya ce, “A gare mu ‘yan APC Yusuf Ata ba dan jam’iyyar APC ba ne. Ba mu ma san dalilin da ya sa aka nada shi minista ba. Duk fadin jihar Kano a karamar hukumarsa ne muka zo na uku a zaben 2023.
“Ba mu san cewa an nada shi minista ba. Mun gaya wa shugaban kasa cewa shi ba dan jam’iyyarmu ba ne. Ya yi wa jam’iyyar zagon kasa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp