Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya halarci taron dandalin tattauna harkokin samar da ci gaba na kasar Sin wato CDF na shekarar 2023, inda ya gabatar da jawabi mai taken “Samun nasarori a sabon tafarkin gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil Adama”.
A cewar Qin Gang, cikin hikima shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kirkiro shawarar gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil Adama, shekaru 10 da suka gabata. Shawarar da ta samar da ka’idoji da alkiblar diflomasiyyar kasar Sin. Ya ce cikin shekaru 10 da suka gabata, an aiwatar da wannan shawara a aikace tare da tabbatar da burinta a zahiri. Haka kuma, ta kasance muhimmin ginshikin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da kara kuzari ga ci gaba a duniya.
Qin ya bayyana cewa, gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil Adama, ta samar da mafitar da Sin ta gabatar ta shawo kan gibin tsaro a duniya, kuma ita ce karfin Sin na ingiza fitar da duniya daga shakkun samun ci gaba da kuma hikimar Sin na ganin ba a samu rikici tsakanin mabambantan al’ummomin duniya ba. (Fa’iza Mustapha)