Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da jakadun kasashen Afirka a kasar Sin, inda suka yi bikin ranar Afirka tare a birnin Beijing.
Jakadu da jami’ai masu kula da harkokin kasashen Afirka fiye da 50 da wakilan Tarayyar Afirka a kasar Sin ne suka halarci bikin.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama A Wani Sabon Hari Da Suka Kai Sansanin Sojoji A Borno
- Gwamnati Ta Kammala Samar Da Fasfo Sama Da 200,000 Da Suka Yi Jinkiri
Wang ya ce, tun bayan shiga sabon zamani, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci kasashen Afirka har sau biyar, ya kuma gabatar da ka’idojin manufofin Sin a Afirka, da suka kunshi gaskiya, da samar da sakamako na hakika, da aminci da yin abu da zuciya guda, da ka’idar neman babban ci gaba mai kyau da moriyar juna, da bin ruhin kawance da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da kuma daukaka dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da dukkan kasashen Afirka zuwa mataki mafi dacewa.
Wang ya yi nuni da cewa, a ko yaushe kasar Sin za ta ba da goyon baya ga tabbatar da matsayin da ya dace na kasashen Afirka bisa adalci, da kuma nuna goyon baya ga Afirka wajen taka muhimmiyar rawa a fagen kasa da kasa.
A nasu bangaren, jakadun kasashen Afirka sun bayyana cewa, jerin kyawawan tsare-tsare na harkokin duniya da ayyukan hadin gwiwa guda 10 da shugaba Xi ya gabatar sun kayatar da kasashen Afirka sosai, kuma sun gamsu matuka da hadin gwiwar da ke tsakanin Afirka da Sin.
Sun kara da cewa, kasashen Afirka za su kafe kai da fata wajen mutunta ka’idar Sin daya tak a duniya, da goyon bayan duk kokarin da kasar Sin ta yi na kare ikon ’yancinta da cimma burin sake hadewar kasar, da yin adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, kana suka ce, kasashen Afirka za su kiyaye manufofi da ka’idojin yarjejeniyar kafa MDD, tare da kare muradu na bai daya na kasashe masu tasowa da kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp