Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashen duniya, wajen yin amfani da shawarwari guda uku na duniya, a matsayin wata dama ta daukaka tafiyar da harkokin teku a duniya, da kyautata jin dadin jama’a.
Wang ya bayyana hakan ne a ranar Talatar nan a wani jawabi kai tsaye ta kafar bidiyo da ya gabatar a wani taron tattaunawa kan yin hadin gwiwa kan harkokin teku da kuma tafiyar da harkokin teku a duniya.
- Muna Bukatar Karin Kudi Don Inganta Ayyukanmu – Hafsan Sojin Kasa
- Jiragen NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Tare Da Tarwatsa Ma’ajiyar Abincinsu A Tafkin Chadi
Yayin da yake tsokaci kan yadda duniya ke fuskantar sabbin damammaki da kalubale a fannin tafiyar da harkokin kasa da kasa, Wang ya ce, sa kaimi ga tafiyar da harkokin teku a duniya da kuma gina al’ummar teku mai makomar bai daya na da muhimmanci wajen gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga kowa.
Ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin da su sa kaimi ga samun bunkasawar teku mai dorewa da inganci, da tabbatar da tsaron teku na duniya kuma dawwamamme, da inganta musayar harkoki masu nasaba da wayewar kai na teku a duniya. (Mohammed Yahaya)