• English
  • Business News
Sunday, September 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministan Najeriya Ya Yi Maraba Da Kamfanonin Sin Da Su Zuba Jari A Kasar

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Ministan Najeriya Ya Yi Maraba Da Kamfanonin Sin Da Su Zuba Jari A Kasar
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Me Ya Sa Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Ta Samu Goyon Baya Daga Sassan Kasa Da Kasa

An Karrama Fitattun Fina-Finai A Bikin “Golden Panda” Da Ya Gudana A Lardin Sichuan Na Kasar Sin

Tarayyar Najeniya, babbar kasuwa ce da kasar Sin take zuba jari, da gudanar da cinikayya, da fitar da kayayyaki, da kuma ayyukan gine-gine a nahiyar Afirka.

Kwanan baya ministan masana’antu da cinikayya da zuba jari na tarayyar Najeriya Otunba Adebayo ya bayyana yayin da ya zanta da wakilin CMG cewa, Najeriya da Sin suna gudanar da hadin gwiwar kut-da-kut a fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwar al’umma da tattalin arziki da cinikayya, kuma Najeriya tana maraba da kamfanonin kasar Sin da su zuba jari tare kuma da kafa kamfanoni a kasar, kana tana fatan za ta yi amfani da damar shiga bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa daga ketare na kasa da kasa na kasar Sin karo na 5 da za a shirya a bana, domin tallata kayayyakin Najeriya ga masu sayayya na kasar Sin.

  • Babban Dan Majalisar Dokokin Kasar Sin Ya Kai Ziyarar Fatan Alheri A Kasar Rasha

Rahotanni sun nuna cewa, gaba daya jimillar darajar cinikayyar dake tsakanin kasar Sin da tarayyar Najeriya a shekarar 2021, ta kai dalar Amurka biliyan 25.68, adadin da ya karu da kaso 33.3 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.

Game da halin da ake ciki a bangaren hadin gwiwar dake tsakanin Najeriya da Sin a fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwar al’umma da tattalin arziki da cinikayya da zuba jari kuwa, minista Adebayo yana mai cewa, tun bayan da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekarar 1971, dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu ta bunkasa daga dukkan fannoni, kuma nan gaba ana sa ran za a ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin Najeriya da Sin zuwa wani sabon matsayi. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

An Kashe ‘Yan Sanda 3, Fararen Hula 3 A Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Sanata Ubah

Next Post

Dalibi Dan Shekara 19 Ya Kashe Kansa A Osun

Related

Me Ya Sa Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Ta Samu Goyon Baya Daga Sassan Kasa Da Kasa
Daga Birnin Sin

Me Ya Sa Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Ta Samu Goyon Baya Daga Sassan Kasa Da Kasa

16 minutes ago
An Karrama Fitattun Fina-Finai A Bikin “Golden Panda” Da Ya Gudana A Lardin Sichuan Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Karrama Fitattun Fina-Finai A Bikin “Golden Panda” Da Ya Gudana A Lardin Sichuan Na Kasar Sin

1 hour ago
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Daga Birnin Sin

An Kama Wani Sojan Gona Ɗauke Da Bindiga A Katsina

3 hours ago
Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya
Daga Birnin Sin

Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

21 hours ago
An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu

23 hours ago
Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok

1 day ago
Next Post
Dalibi Dan Shekara 19 Ya Kashe Kansa A Osun

Dalibi Dan Shekara 19 Ya Kashe Kansa A Osun

LABARAI MASU NASABA

Me Ya Sa Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Ta Samu Goyon Baya Daga Sassan Kasa Da Kasa

Me Ya Sa Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Ta Samu Goyon Baya Daga Sassan Kasa Da Kasa

September 14, 2025
Sama Da Fam Biliyan Uku Aka Kashe A Firimiyar Ingila Wajen Sayen Ƴan Wasa

Sama Da Fam Biliyan Uku Aka Kashe A Firimiyar Ingila Wajen Sayen Ƴan Wasa

September 14, 2025
Me Ya Sa Bayern Liverkusen Ta Kori Erik Ten Hag Bayan Wasanni Biyu?

Me Ya Sa Bayern Liverkusen Ta Kori Erik Ten Hag Bayan Wasanni Biyu?

September 14, 2025
An Karrama Fitattun Fina-Finai A Bikin “Golden Panda” Da Ya Gudana A Lardin Sichuan Na Kasar Sin

An Karrama Fitattun Fina-Finai A Bikin “Golden Panda” Da Ya Gudana A Lardin Sichuan Na Kasar Sin

September 14, 2025
Matashi Ya Rasa Ransa A Yunƙurin Satar Kyabul Ɗin Taransifoma A Maiduguri

Matashi Ya Rasa Ransa A Yunƙurin Satar Kyabul Ɗin Taransifoma A Maiduguri

September 14, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

An Kama Wani Sojan Gona Ɗauke Da Bindiga A Katsina

September 14, 2025
Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina

NPA Ta Fara Aiki Da Sabon Tsarin ETO A Tashar Apapa

September 14, 2025
Sojojin Nijeriya Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 139, Sun Cafke 132 A Cikin Sati 2 —Hedikwatar Tsaro

Sojoji Sun Ceto Mutane 30 Da Aka Yi Garkuwa Da Su, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama

September 14, 2025
Ɗalibai 750 Sun Amfana Da Bashin Karatu Na Naira Milyan 32.14 A Jihar Gombe

Ɗalibai 750 Sun Amfana Da Bashin Karatu Na Naira Milyan 32.14 A Jihar Gombe

September 14, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Ceto Yara 5 Da Aka Sace A Adamawa

September 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.