Ministan ilimi, kimiyya da fasaha na kasar Tanzania Adolf Mkenda ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gajiyar hadin gwiwar koyar da fasahohi da ilmomin sana’o’i wato TVET da kasar Sin, wajen bai wa daliban da suka kammala karatunsu a wannan fanni, damar cimma matsayin da ake bukata a gida da kuma kasa da kasa.
Ministan ya bayyana cewa, ana sa ran raba kwarewar da kasar Sin ta cimma, za ta yi tasiri mai kyau kan farfadowa da bunkasuwar tsarin TVET a kasar Tanzania.
Mkenda ya bayyana hakan ne Juma’ar da ta gabata, lokacin da yake bude taron yini guda na hadin gwiwa da musayar ilimi tsakanin kasashen Sin da Afirka, da aka gudanar a makarantar koyon shugabanci ta Mwalimu Julius Nyerere da ke gundumar Kibaha a yankin gabar teku. (Mai fassara: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp