Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da takwansa na Mali Abdoulaye Diop a jiya Juma’a, inda yayin tattaunawar tasu ya ce Sin ta kuduri aniyar bunkasa hadin gwiwa da Mali, a fannonin raya ilimi, da horaswa, da kiwon lafiya da noma.
Wang ya ce Sin da Mali na da dadadden zumunci, wanda tsofaffin shugabanninsu suka kafa, kuma Sin ta fahimci Mali, tana kuma girmama ‘yancin kasar da zabin al’ummar ta, kana ba za ta taba tsoma baki cikin harkokin gidan Malin ba.
- Sin: Ya Kamata Kwamitin Sulhu Ya Kara Daukar Matakai Kan Lokaci Don Inganta Tsagaita Bude Wuta Da Kawo Karshen Yaki A Dukkan Fannoni
- Gwamnan Kano Zai Gana Da Shugaban ‘Yan Fansho Kan Batan Naira Biliyan 5
Kaza lika, Sin ta gamsu cewa, Mali na da dabaru, da ikon warware wahalhalu na dan lokaci da take ciki, za ta kuma kai ga cimma burin bunkasa kasa, da samar da ci gaba da kan ta, har ta kai ga samun cikakken yanayin zaman lafiya da lumana.
Wang, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da Mali, ta yadda za su goyawa juna baya, su kare halastattun hakkoki, da moriyar kasashe masu tasowa, kana su kare ka’idojin cudanyar kasa da kasa.
A nasa tsokaci kuwa, mista Diop ya ce Sin da Mali sun dade suna kawance, kuma suna da matsaya guda kan muhimman batutuwa dake shafar su, kuma Sin abokiyar hulda ce da Mali ke iya dogaro da ita. Ya kara da cewa, Mali na nacewa manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, tana kuma fatan zurfafa hadin gwiwar cimma moriyar juna tare da Sin, da koyi daga kwarewar Sin a fannin cimma nasarorin bunkasa kasa. (Saminu Alhassan)