Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya musanta zargin da ake yi cewa, wai kasar Sin na haifar da “tarkon bashi” a Afirka, yana mai cewa, abin da ake kira wai tarkon bashi, magana ce maras tushe da aka kirkira kan kasar Sin da Afirka.
Qin ya bayyana hakan ne, a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp