A jiya Asabar, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da manyan jami’an kasashen Jamus, da Faransa, da Isra’ila, da Ukraine, da sauransu, a birnin Munich na kasar Jamus.
Yayin ganawarsa da shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz, mista Wang Yi ya ce, kasar Sin na son zurfafa hadin kai daga dukkan fannoni tare da kasar Jamus, don tabbatar da kyautatar huldar kasashen 2, da samun kwanciyar hankali a duniya. Kana a nasa bangare, mista Olaf Scholz ya ce kasar Jamus ba ta yarda da yunkurin ta da “yakin harajin kwastam” a duniya ba, kuma tana fatan ganin bangarorin Turai da Sin su cimma matsaya cikin sauri, wajen daidaita sabanin ra’ayinsu ta fuskar cinikayyar motoci masu amfani da wutar lantarki.
- Tinubu Ya Buƙaci A Mayar Wa BUK Filin Rimin Zakara Da Ake Taƙaddama A Kai
- Kishin Ƙasa Da Tsoron Allah Ne Mafita Daga Matsin Tattalin Arziƙin Ƙasar Nan – Malam Usman
Sa’an nan, duk a jiya Asabar din, Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Faransa, Jean-Noel Barrot, inda bangarorin 2 suka amince da karfafa hadin gwiwar kasashensu kan batun kula da al’amuran duniya, da ingiza hadin kan kasashen duniya a kokarin tinkarar kalubalolin da dan Adam ke fuskanta.
Ban da haka, yayin da yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar Isra’ila Gideon Sa’ar, minista Wang Yi ya ce, mafitar da ake da ita wajen daidaita batun Gabas ta Tsakiya, ta shafi aiwatar da manufar tabbatar da wanzuwar kasashe 2, wato Isra’ila da Falasdinu, a yankin da suke ciki, ta yadda za a cimma burin kasancewar kasashen 2 cikin lumana a karshe. A nata bangare, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin kare adalci, da samar da gudunmowa ga aikin daidaita maganar Falasdinu daga tushenta, in ji mista Wang.
Haka zalika, a lokacin da yake ganawa da Andriy Sybiga, ministan harkokin wajen kasar Ukraine, Wang Yi ya ce, kungiyar “Abokan zaman lafiya” da Sin da sauran kasashe masu tasowa suka kafa, za ta ci gaba da taka rawar gani, a kokarin kawo karshen yakin da ake yi a Ukraine ta hanyar sulhuntawa da shawarwari.
Har ila yau a jiya Asabar, Wang Yi ya kuma gana da jami’an kasahen Brazil, da Czech, gami da Austria. (Bello Wang)