Jiya Talata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya taya wa takwaransa na Najeriya Yusuf Maitama Tugar murnar kama aiki ta wayar tarho.
Wang Yi ya ce, Sin da Najeriya manyan kasashe masu tasowa ne, tun kulla huldar diflomasiyya tsakaninsu cikin shekaru 50 da suka gabata, bangarorin biyu sun tsayin daka kan mutunta juna da cin moriya tare cikin adalci, da ma kara inganta amincewa tsakaninsu ta fuskar siyasa, da ingiza hadin kan bangarorin biyu a fannin manyan ababen more rayuwa da sha’anin noma da sadarwa da hada-hadar kudi da sauransu, matakin da ya ba da jagoranci ga hadin kan Sin da Afrika. Wang Yi yana mai fatan kafa hulda mai nagarta tsakaninsu don zurfafa hadin kan kasashen biyu a fannnoni daban-daban bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon matsayi. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp