Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya (NPF) da ta rungumi Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa.
Ya bayyana cewa, rungumar ƙa’idojin Yarjejeniyar zai inganta kallo da fahimtar da jama’a suke yi wa rundunar.
- Xi Ya Yi Kiran Gina Duniya Mai Ci Gaba Ta Bai Daya Bisa Adalci A Taron G20
- An Fara Watsa Shirin Zababbun Kalaman Da Shugaba Xi Jinping Ya Fi Kauna A Kasar Brazil
Sanarwar da Mataimaki na Musamman ga Ministan kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabiu Ibrahim, ya fitar ta nuna cewa ministan ya bayyana hakan ne a yayin wani taron ƙara wa juna sani na jami’an hulɗa da jama’a na ‘yan sanda wanda aka yi a Asaba, Jihar Delta.
Idris, wanda ya samu wakilcin Darakta-Janar na gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba-Ndace, ya ce: “An ƙirƙiri Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa a matsayin tsarin ayyana mu a matsayin ’yan Nijeriya da kuma tabbatar da manufofin mu na gaskiya a cikin muradin mu.
“Tana cike giɓin da aka samu wajen neman haɗin kan ƙasa, cigaban al’umma, da kishin ƙasa mai ɗorewa a tsakanin ‘yan Nijeriya.
“Don haka ina amfani da wannan dama don yin kira ga Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya da ta rungumi yarjejeniyar ɗa’ar da zuciya ɗaya, tare da yin amfani da ita don ƙirƙirar sabon labari na Nijeriya.
“Dole ne dukkan mu mu gane cewa ‘Yan Sandan Nijeriya na kan gaba wajen yadda ake kallon ƙasar mu a cikin ƙasa da kuma duniya.”
Ministan ya bayyana irin rawar da ‘yan sanda ke takawa a matsayin hukumar tsaro ta farko da ke mu’amala da al’ummar Nijeriya.
Ya yi nuni da cewa aikin rundunar ya wuce tabbatar da bin doka da oda, ya kai ga kare rayuka, mutunci, ‘yanci, da dukiyoyin ‘yan ƙasa, inda ya jaddada muhimmancin yin aiki da kundin tsarin mulki da kuma yarjejeniyar zamantakewa da ‘yan ƙasa.
Ya ƙara da cewa aikin ‘yan sanda mai inganci ya dogara ne da fahimtar juna da kuma wani nauyi da ya rataya a wuyan ‘yan sanda, gwamnati, da jama’a, yana mai cewa amanar jama’a ita ce ƙalubale mafi girma da rundunar take fuskanta a yau.
Ya ce: “A cigaban da muke samu a matsayin mu na ƙasa da kuma cigaban mutuncin mu, ‘yan sanda sun yi fafutuka wajen mu’amala da jama’a, musamman saboda saɓani na kare haƙƙin jama’a da tabbatar da zaman lafiya a ƙasar.
“Wannan gwagwarmaya ta ƙara zama ƙalubale saboda akwai wasu abubuwan cikin gida masu hani da ke dagula tasirin ƙwararrun ‘yan sanda wajen gudanar da ayyukan su.”
Ministan ya yaba wa shugabannin NPF da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, bisa shirya taron.
Ya kuma amince da daidaita ayyukan rundunar tare da manufar Shugaba Bola Tinubu ta samun ingantaccen aiki.