Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa Hukumar Sayen Kayayyaki ta Ƙasa (BPP) kan ƙoƙarin ta na inganta gaskiya da riƙon amana a wajen sayen kayayyaki da bayar da kwangiloli.
A wata ganawa da ya yi a Abuja a ranar Alhamis tare da Babban Daraktan BPP, Dakta Adebowale Adedokun, da wasu shugabannin hukumar, Idris ya jinjina wa ƙoƙarin hukumar na sauƙaƙa tsarin sayan kayayyaki.
- Sojoji Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda, Sun Kama Masu Safarar Makamai, Sun Ceto Mutane
- ‘Yan Nijeriya Za Su Maka Gwamnati A Kotu Kan Karin Kudin Kiran Waya
Ya nanata jajircewar Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata na tabbatar da gaskiya wajen bayar da kwangiloli.
Ya ce: “Kafin yanzu, ana ɓoye-ɓoye wajen sayen kayayyaki sau da yawa. Ina farin cikin cewa kuna bayyana komai yanzu. Babu abin da ya kamata a ɓoye. Idan wannan kamfani ya samu kwangila, a bari kowa ya sani cewa wannan kamfani ya samu kwangilar kuma waɗannan su ne dalilan. Idan aka ci gaba da wannan bayyana gaskiyar da hukumar ku ke yi, to zan iya tabbatar maku da cewa idan mutum ya rasa wata kwangila ba zai yi baƙin ciki ba.”
Idris ya bayyana sabon tsarin BPP na kammala sayen kayayyaki cikin kwana 20 a matsayin wani babban cigaba wanda ke nuna ƙwaƙƙwaran jagoranci da sha’awar kawo gyara.
Ya ƙara da cewa ingantaccen tsarin sayen kayayyaki zai taimaka wajen adana albarkatu don kawar da talauci a ƙasa.
Ministan ya kuma tabbatar da cewa ma’aikatar sa za ta haɗa kai da BPP wajen wayar da kan jama’a kan tsarin sayen kayayyaki da kuma yaƙi da lalata kayan gwamnati.
Ya kuma bayyana cewa an sauya sunan ma’aikatar sa zuwa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ne domin a mayar da hankali kan wayar da kan jama’a da dawo da ƙimar ƙasa.
Ya ce: “Abin da Shugaban Ƙasa ke ƙoƙarin faɗi shi ne cewa akwai sabon mayar da hankali kan wayar da kai da dawo da darajar ƙasa, kuma Shugaban Ƙasa zai ƙaddamar da Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa nan ba da jimawa ba a madadin ’yan Nijeriya.”
A nasa ɓangaren, Babban Daraktan jukumar ta BPP, Dakta Adebowale Adedokun, ya jaddada ƙoƙarin hukumar na aiwatar da tsarin sayen kayayyaki mai gaskiya da adalci.
Ya bayyana cewa dole ne dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati su kammala sayen kayayyaki kafin ƙarshen rabin shekara.
Dakta Adedokun ya sanar da cewa hukumar tana komawa tsarin sayen kayayyaki na onlayin don bai wa masu kwangila daga sassa daban-daban na ƙasa da ƙetare damar shiga tsarin.
Ya kuma ce an fara tantance masu ba da shawara da masu ba da sabis don taimaka wa ‘yan kwangilar gida su iya yin gasa a yadda ake yi a ko’ina a duniya.
Domin inganta gaskiya, ya ce dole ne ma’aikatu da hukumomin gwamnati su gabatar da rahotannin kwata-kwata na kwangilolin da aka bayar, ciki har da sunayen ‘yan kwangilar, waɗanda za a wallafa su a gidan yanar BPP.
Haka kuma an samar da sababbin ƙa’idojin sayen kayayyakin aikin asibiti, tsaro na abinci, da motoci don tabbatar da daidaiton tsarin.