• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Jimamin Rasuwar Babban Ɗan Jarida Leon Usigbe

by Sulaiman
2 months ago
Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana alhinin sa kan rasuwar fitaccen ɗan jaridar nan, Dakta Leon Habby Usigbe, wanda ya kasance shugaban jaridar Nigerian Tribune a Abuja.

A cikin wata sanarwa ta ta’aziyya da ya fitar a ranar Asabar, 26 ga Yuli, 2025, Ministan ya bayyana marigayin a matsayin “ɗan jarida na ƙwarai, ƙwararre mai kaifin basira, kuma haske a fagen aikin jarida a Nijeriya.”

  • Ƴansanda Sun Cafke Barayin Motoci 3 A Kano
  • Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu

Ya ce ayyukan Usigbe sun bayyana gaskiyar sa, zurfin sa a tunani, da jajircewar sa wajen kare muradun jama’a.

Ya ce: “A matsayin sa na ɗan jarida mai amfani da alƙalamin sa wajen kare dimokiraɗiyya da cigaban ƙasa, ya riƙa kawo bayanai masu zurfi, ilimi, da daidaito a cikin rahotannin sa. A cikin sa, ‘yan jarida sun samu ɗan ƙasa nagari wanda ya yi amfani da sana’ar sa wajen bunƙasa gaskiya da cigaban ƙasa.”

Idris ya kuma tuna yadda Usigbe ya riƙa bayar da gagarumar gudunmawa a tarukan manema labarai da ma a Fadar Shugaban Ƙasa, yana cewa, “Shiga tsakani da ya riƙa yi a irin waɗannan taruka na manema labarai na haɓaka ingancin muhawara, ya kuma taimaka wajen ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnati da ‘yan jarida — duk da nufin samar da al’umma mai wayewa tare da fahimtar juna.”

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

Ya ce rasuwar Dakta Usigbe babban rashi ne ba kawai ga kamfanin jaridar Tribune da fagen aikin jarida ba, har ma da ƙasar nan baki ɗaya.

“Nijeriya ta yi rashi matuƙa — mun rasa ɗaya daga cikin fitattun ‘yan jarida, wanda ilimin sa, jarumtar sa, da himmar sa ta sa kowa yana girmama shi.”

A madadin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Idris ya miƙa ta’aziyyar sa ga shugabanni da ma’aikatan Tribune, da gwamnati da al’ummar Jihar Edo inda marigayin ya fito, da kuma iyalan sa, da abokan sa, da ma dukkan masu mu’amala da shi.

“Allah ya jiƙan sa, ya ba duka waɗanda ya bari haƙurin jure wannan babban rashi,” inji Ministan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI
Labarai

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC
Labarai

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Next Post
Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno

Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

October 9, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.