A yau Alhamis ne ministocin wajen kasashen Sin, da Rasha, da Pakistan da Iran, suka tattauna a karo na 2 game da batun kasar Afghanistan.
Yayin taron da ya gudana a Uzbekistan, wanda kuma ministan harkokin wajen Sin Qin Gang ya jagoranta, manyan jami’an jakadancin kasashen sun cimma matsaya da dama, ciki har da kira ga Amurka da ta dage takunkumin kashin kai da ta kakabawa Afghanistan, a hannu guda kuma sun yi kira ga mahukuntan Afghanistan da su kafa gwamnatin da za ta kunshi dukkanin sassan kasar, wadda kuma za ta kare moriyar daukacin al’ummar kasar ciki har da mata, da yara, da al’ummun kananan kabilun kasar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp