Shugaban Miyetti-Allah Cattle Breaders na kasa, Alhaji Hussaini Yusuf Bosso (Jarman Chibi) ya nemi shugabannin kungiyoyin Fulani da sarakuna da su kara kaimi wajen wayar da kan makiyaya muhimmancin mallakar katin zabe.
Shugaban ya yi kiran ne lokacin da yake karin haske ga manema labarai kan muhimmancin mallakar katin zabe. Ya ce zama wajibi duk makiyayi ya tabbatar ya mallaki katin zabe a inda yake zama muddin ya kai shekarun jefa kuri’a.
A cewarsa, mallakar wannan katin shi ne kawai zai tabbatar da kai a matsayin dan kasa mai ‘yanci da zai iya zaben shugabanni masu zuwa, idan mutum bai yi zabe ba, bai da ‘yancin yin korafi ko kokawa a kan rashin daidai da yake zargin an masa.
Ya ce shugabannin kungiyoyin Fulani a duk inda suke da sarakunansu su tashi tsaye wajen wayar da kan makiyaya muhimmancin mallakar katin nan, akwai dubban makiyaya a cikin karkaru da ke bukatar karin haske da wayar da kai musamman sanin wuraren da ya kamata a mallaki katin zaben.
Shugaban ya nemi ‘yan siyasa da su ji tsoron Allah su rika cika alkawurran da suka dauka a lokacin yakin neman zabe. Ya ce kasar nan muna neman shugabanni jajirtattu da za su iya hada kan ‘yan kasa domin kawar da matsalolin da kasar nan ke fama da su.