Mizanin kayan masarufi na kasar Sin (CPI), wanda yake babban ma’aunin hauhawar farashin kayayyaki, ya karu da kashi 0.2% a mizanin shekara-shekara na watan Oktoban shekarar 2025, kamar yadda bayanai daga Hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) suka nuna a yau Lahadi.
Har ila yau, a cewar bayanan, a kididdigar kowane wata, mizanin na CPI ya karu da kashi 0.2% a watan da ya gabata.
Babban ma’aunin bayanai na mizanin CPI kuma, wanda bai kunshi farashin abinci da makamashi ba, ya karu da kashi 1.2% a mizanin shekara-shekara, wanda ke nuna ci gaban da aka samu cikin hanzari a tsakanin watanni shida a jere.
Jami’ar hukumar ta NBS madam Dong Lijuan ta danganta karuwar farashin kayan masarufin a watan da ya gabata bisa tasirin da manufofin fadada bukatun cikin gida ke ci gaba da yi, tare da karuwar tasirin hutun murnar bikin kafuwar Jamhuriyar jama’ar kasar Sin da na Tsakiyar Kaka wato Zhongqiu da aka yi.
Bayanan na yau Lahadi, sun kuma nuna cewa ma’aunin farashin samar da kayayyaki (PPI), wanda ke auna farashin kayan kamfanin kafin fitarwa zuwa kasuwa ya ragu da kashi 2.1 cikin dari a bisa mizanin shekara-shekara da aka auna a watan Oktoba.
Dong ta danganta raguwar farashin na PPI da aka samu a mizanin shekara-shekara bisa karuwar yawan sarrafa kaya a manyan masana’antu, da hanzarta kokarin kafa masana’antu na zamani, da kuma bude hanyoyin sayayyar kayayyaki.
A watan Oktoba, ci gaban da aka samu na karuwar hada-hadar kaya da bukatarsu ya haifar da hauhawar farashi a wasu sassa kamar masana’antar hakar kwal da sarrafa shi, kamar yadda Dong ta bayyana, yana mai nuni da cewa su ma sauye-sauyen farashi a kasashen duniya sun shafi farashin wasu kayan masana’antun cikin gida. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














