• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

MOFA: Batun Taiwan Ba Ya Bukatar Tsangwama Daga Waje

by CGTN Hausa
1 year ago
MOFA

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya fada a wata hira da ya yi cewa, idan aka samu rikici na soji tsakanin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan, bai kawar da yiwuwar shiga tsakani na sojojin Amurka ba. Dangane da hakan, yayin da take mayar da martani, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labarai da aka saba gudanarwa a yau 5 ga wata cewa, Taiwan wani yanki ne da ba zai taba rabuwa da kasar Sin ba, kuma batun Taiwan lamari ne na cikin gida na kasar Sin wanda ba ya lamuntar tsoma baki daga waje.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Sun Weidong zai jagoranci wata tawaga da za ta halarci taron manyan jami’an ASEAN da Sin da Japan da Koriya ta Kudu, da taron manyan jami’ai na gabashin Asiya, da taron manyan jami’ai na dandalin tattaunawar ASEAN da za a yi a Vientiane a ranar 7 zuwa 8 ga wata. Mao Ning ta kara da cewa, kasar Sin na fatan yin mu’amala mai zurfi tare da dukkan bangarorin da za su halarci tarukan, domin sa kaimi ga samun sabbin ci gaba a hadin gwiwar dake tsakanin kasashen gabashin Asiya, da ba da gudummawa sosai wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun ci gaba tare.

  • Sin Tana Son Yin Aiki Tare Da Hukumar IAEA Don Tabbatar Da Shawarar Ci Gaban Duniya Da Shawarar Tsaron Duniya
  • Wang Yi: Karin Kasashe Na Nuna Goyon Baya, Za A Kyautata Fatan Samun Zaman Lafiya

Ban da haka kuma, kasar Sin ta taya firaministan kasar Indiya Narendra Modi murnar samun nasara a zaben kasar, a cewar Mao Ning. Ta kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Indiya wajen ci gaba da tabbatar da moriyar kasashen biyu da al’ummominsu, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar huldar dake tsakanin kasashen biyu bisa turba mai inganci da kwanciyar hankali.

Kasar Sin ta kuduri aniyar wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsibirin Koriya, kuma tana adawa da duk wata magana ko aiki da ke kara ta’azzara rikici a tsibirin, a cewar Mao Ning biyo bayan shawarar da kasar Koriya ta Kudu ta yanke ta dakatar da yarjejeniyar soja da kasar Koriya ta Arewa da ita suka daddale a ranar 19 ga watan Satumban shekarar 2018. (Yahaya)

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 17, 2025
Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika
Daga Birnin Sin

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Next Post
Zargin Da Ke Tattare Da Kalaman Da ‘Yan Siyasar Philippines Ke Yi Kan Kasar Sin

Zargin Da Ke Tattare Da Kalaman Da ‘Yan Siyasar Philippines Ke Yi Kan Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 17, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

Zan Tabbatar Ana Tafiyar Da Ayyuka A Tashoshin Jiragen Ruwa A Afrika Ta Yamma —Dantsoho

October 17, 2025
Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

October 17, 2025
peter

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

October 17, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

October 17, 2025
Tinubu

Batun Yin Afuwa Ga ‘Yan Yankin Ogoni Huɗu

October 17, 2025
Shettima

‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima 

October 17, 2025
Manzon Allah

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

October 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.