A kwanakin baya ne, aka kammala taron kolin shugabannin kasashen Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin da Afirka ta kudu (BRICS).
Duk da cewa taron ya gudana ta kafar bidiyo, amma hakan bai hana shi cimma manyan sakamako da zai amfanawa kasashen da ma duniya baki daya ba.
A duk lokacin da aka ambaci kungiyar, abin da mutum zai yi tunani shi ne, yadda manufofi da tsare-tsarenta za su amfani daukacin bil-Adama.
Bayanai na nuna cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen kungiyar BRICS ya kai matsayin koli, har ma an samu muhimman nasarori 10 a bangarori daban daban.
Wannan shi ne abin da ake bukata daga kowace kungiya, sabanin yadda taron G7 ke neman bata sunan shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta hanyar bullo da wani shiri, wai raya duniya da sunan samarwa kasashe masu tasowa kayayyakin more rayuwa. Sai dai dadin bakin su ba zai yaudari sauran kasashe ba.
Ya zuwa yanzu, kungiyar BRICS ta kai ga samun manyan sakamakon da yawansu ya kai 37 a bana, kana nasarori goma da kasashen suka samu, sun hada da: nacewa kan tabbatar da adalci tsakanin kasa da kasa ta hanyar fitar da “sanarwar Beijing”, da inganta aikin dakile annobar cutar COVID-19 ta hanyar kafa “cibiyar nazarin allurar rigakafin cutar ta kasashen BRICS”, da ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba, da kara karfafa aikin yaki da cin hanci da rashawa, da kafa babbar kasuwar da ta dinke kasashen BRICS, da kokarin tabbatar da aikin samar da isasshen abinci ga al’ummomin kasa da kasa, da amfani da boyayyen karfin kirkire-kirkire domin samun ci gaba tare, da kara habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen mambobin kungiyar a bangaren kimiyya da fasaha ta zamani, da amfani da damammakin raya tattalin arziki ta yanar gizo a sabon zamanin da ake ciki, da kuma horas da masana fasahohi, ta yadda za a samu ci gaba mai dorewa a nan gaba.
Abin da duniya ke bukata, shi ne sakamako na zahiri, ba maganar fatar baki ba. Domin yanzu kan mage ya waye. (Ibrahim Yaya)