A ’yan kwanakin baya na samu zarafin ziyartar jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kai dake arewacin kasar Sin. Jiha ce mai tsayin kusan kilomita 2,900 da ta hade sassan yankunan arewaci da arewa maso gabashin kasar Sin, wanda kuma ke da tsaunuka, da tuddai, da kwazazzabai, da makiyaya mai kayatarwa.
Hamadar Gobi na yankin jihar ta arewa, kana kan iyakar jihar ta kudu na hade da Babbar Ganuwar kasar Sin, yayin da hamadar Kubuqi ke a sashen birnin Ordos, na jihar. Bisa abubuwan da idanuna suka gani na lura cewa gwamnatin kasar Sin da jama’ar wannan jaha sun yi namijin kokari wajen raya dukkanin sassan ci gaba bisa fifikon da jihar ke da shi na fadin kasa, da makiyaya mai girma, da albarkar noma, da ruwa, da kwazazzabai da tuddai, har ma da babbar hamadar dake wannan jiha wajen bunkasa tattalin arzikin noma da kiwo, da bunkasa harkar samar da makamashi mai tsafta da yawon shakatawa.
- Fahimtar Manufar Kasar Sin Ta Yin Kwaskwarima A Sabon Zamani
- Peng Liyuan Ta Yi Kira Da Karin Hadin Gwiwa Tsakanin Kasa Da Kasa Domin Takaita Cututtukan Kanjamau Da Tarin Fuka
Tun daga saukarmu a birnin Ulanqab na jihar ta Mongolia ta gida muka yada zango a kauyen Hua, na garin Pingdiquan, inda muka ziyarci wani gida da ake kira “Gidan Farin Ciki”, wanda aka tanada musamman domin warware matsalar tsofaffi mazauna kauyen masu bukatar kulawa da matsuguni saboda rashin galihu, ko rashin wadanda za su iya kulawa da su yau da kullum. “Gidan Farin Ciki” na da dakuna irin na kwanan dalibai ’yan makaranta masu tsafta reras bisa tsari, da dakunan cin abinci, da dakunan gudanar da sauran abubuwan rayuwa daban daban. An tanadi ruwa mai dumi ta amfani da na’urar dumama ruwa mai aiki da hasken rana, ga kuma dakunan kwantar da marasa lafiya idan bukatar hakan ta taso. Duka dai domin tsofaffin dake da rangwamen gata dake kauyen su samu matsugunni mai kyau, wanda zai samar musu da farin ciki da walwala.
Gidan Farin Ciki, na samar da nau’o’in tallafi a fannoni 7 ga tsofaffin wannan kauye: akwai rangwamen kudin sayen abinci, da na magani, da na wanki, da wanka, da sayen kayan masarufi, da karatun jami’a na tsofaffi, da hidimomin motsa jiki. Tsofaffin dake wannan kauye na rayuwa cike da farin ciki sakamakon tallafin da suke samu daga masu kula da su a wannan gida na musamman.
Daga nan kuma sai kauyen Nancun dake garin Pingdiquan a dai birnin na Ulanqab. A wannan kauye an samar da wani tsari tattara manyan bayanai, da hade bayanai game da albarkatun irin shuka da ake da su wuri guda. Akwai cibiyoyin ilmantar da matasa harkokin kwadago, da sauran ayyukan da aka tsara domin bunkasa noma, da sanin makamar aiki a fannin sana’ar ta noma. Wannan tsari ya yi matukar inganta aikin farfado da kauyen, ya kuma lashe manyan lambobin yabo na kasa cikin shekaru biyu da suka gabata.
A kauyen Nancun na garin Pingdiquan, an yi amfani da albarkatun dake akwai wajen samar da kauye mai kyaun gani, da kayatarwa, tare da bunkasa yankin raya harkokin noma, da yankin nuna kimiyya da fasahohin noma, inda har aka ware wasu gonakin gwaji na tsinkar ’ya’yan itatuwa da kayan lambu, da na kallon albarkatun gona a matsayin fannin yawon bude ido ga masu sha’awa.
Har ila yau, da almurun kowace rana, akwai wata unguwa mai kasuwar dake ci da dare a birnin na Ulanqab. Masu yawon bude ido kan ziyarci wannan kasuwa domin kallon wasannin nuna fasahohi daban daban, da daukar hotuna, kana da ziyartar kantunan ta masu cike da hajojin al’adun gargajiya da na fasahohin hannu, tare da dandana nau’o’in abincin birnin Ulanqab.
A fannin kiwon lafiya, asibiti na 3 na birnin Ulanqab, na aiwatar da wani salon a musamman, inda yake yin hadin gwiwa tare da kungiyar kwararru ta ba da hidimomin kiwon lafiya na zamani mai suna “Beijing Ivy Medical High-end Talent Alliance”. Ta wannan hadin gwiwa da kungiyar, wasu kwararrun likitoci daga birnin Beijing, ciki har da wadanda suka yi ritaya daga aiki na zuwa asibitin domin duba marasa lafiya, kuma ta hakan mazauna birnin Ulanqab sun samu damar cin gajiyar ingantattun hidimomin kiwon lafiya irin na manyan asibitocin birnin Beijing, ba tare da yin tafiya mai nisa ba.
Wata sana’a mai kayatarwa da na ga wasu dattawa mazauna wannan birni na gudanarwa ita ce fasahar amfani da gashin dabbobi domin fitar da surar halittu daban daban kan wasu kyallaye da yaduka, ta yadda gashin da aka yi amfani da shi zai fitar sa surar dabbar da aka tsara kan kyallen tamkar ta gaske. Bayan kammala aikin, jama’a na sayan wadannan ayyuka domin kyan ganin su a matsayin abubuwan kawata wuraren zama. A shekarar 2021, an shigar da wannan fasaha cikin fasahohin gado na kasa, wadanda ba na kaya ba da aka gada daga kaka da kakanni. Kuma sana’ar ta samar da zarafi na raya tattalin arzikin masu gudanar da ita, baya ga jan ra’ayin ’yan yawon bude ido da take yi a ko da yaushe.
Cikin wurare da suka fi ba ni sha’awa yayin wannan ziyara akwai yankin duwatsu da suka taba yin aman wuta dake birnin Ulanqab, yanki ne dake can tsakiyar tsandaurin Chayouhou. Wuri ne sananne a kasar Sin wanda ya shahara ta fannin yawon shakatawa, da masu zuwa hutu. Ana fatan ya zuwa shekarar 2025 za a daga matsayinsa zuwa wuri mai jan hankalin ’yan yawon bude ido mafi girman daraja ko “5A-level tourist attraction” a Turance, wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa farfado da yankin karkarar wurin, da ingiza ci gaban tattalin arziki mai inganci a yankin. A kan hanyar zuwa wannan yanki ana iya hango manyan tsaunuka da dama da suka taba yin amon wuta daruruwan shekaru da suka gabata, wadanda yanzu ’yan yawon bude ido suka mayar wuraren kashe kwarkwatar idanu da shakatawa.
A can gaba kuma sai filin ciyayi na Huanghuagou dake birnin na Ulanqab, wanda daya ne daga irin wadannan makiyaya guda uku da ake da su a duniya, saboda nau’o’in ciyayi na musamman dake akwai a wurin da kuma tudunsa. Kaza lika, makiyayar ita ce mafi kusa da birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin. A lokutan da aka fi zuwa ziyara wannan makiyaya, wato lokacin zafi, yanayin samaniyar wurin na cike da fararen gajimare da launin shudi, ga ciyayi ko ina kore shar, da furanni, da shanu, da tumaki, da awaki da rakuma da dawaki suna kiwo, yanayin dake samar da mishadi na kallon wuri mai ban sha’awa tamkar wata aljannar duniya.
Daga makiyayar Huanghuagou sai kauyen Ruquan, inda a shekarar 2017 aka samar da wata masa’antar sarrafa madara domin bunkasa tattalin arziki. A wannan masana’anta ana amfani ne da tsarin gargajiya inda ake sarrafa cukui, da awarar madara, da “butter”, da sauran su duka da hannu. Kayayyakin da ake sarrafawa a masana’antar suna samun karin karbuwa ga masu sayayya, saboda ingancin su ta fuskar gina jiki, da dandano mai dadi na musamman. A lokaci guda kuma, masana’antar tana kara fadada hanyoyin sayar da kayayyakinta ta tallatawa da sayar da su ta tallace-tallace kai tsaye a kafofin cinikayya na yanar gizo, wanda hakan ke ingiza manufar farfado da kauyen, yayin da kuma manoma da makiyaya da dama ke samun karin kudaden shiga sanadiyyar hakan.
Baya ga masana’antar sarrafa madara ta kauyen Ruquan, mun kuwa ziyarci wata masana’antar sarrafa hatsin oat, wadda ke gudanar da ayyuka daban daban, tun daga renon irin hatsin, da shuka adadi mai yawa, da sarrafa hatsin bayan ya nuna. Kana da sayar da abubuwan da ake sarrafawa daga hatsin na oat a masana’antar. Tun kafuwar kamfanin, ya dauki mazauna yankin sama da 400 aiki, wadanda suke samun kudaden albashi mai tsoka, matakin da ya raya tattalin arziki da bunkasa kudaden shigar manoma da makiyayan wurin.
Daga birnin Ulanqab sai birnin Ordos, inda muka ziyarci yankin Dalad, wurin da ake aiwatar da katafaren aikin samar da lantarki ta amfani da hasken rana. Yankin yana tsakiyar sashen hamadar Kubuqi ne a birnin Ordos, kuma ya kunshi cikakkun tsare-tsaren bunkasa samar da makamashi da fasahohin farfado da muhallin halittu, inda karkashin hakan aka kai ga kyautata fadin wurin da ya kai sama da eka 300,000 na hamadar Kubuqi, matakin da ya taka muhimmiyar rawa wajen cimma manufar Dalad ta kyautata tsarin samar da makamashi a jihar Mongolia ta gida, tare da ingiza gudanar da ayyukan kare muhallin halittu a hamadar Kubuqi.
A dai wannan yanki na Dalad akwai sashen Yinkentala, babban yanki ne na nune nunen fasahohin kare muhalli. Tun a shekarar 2000 a yankin na Yinkentala aka fara aiwatar da manufar da aka yiwa lakabi da “Three Norths”, wato aikin samar da shingen bishiyoyi da aka karkasa zango-zango, da nufin tabbatar da kara kyautata muhallin halittu, da cimma nasarar bunkasuwa daga dukkanin fannoni, kama daga habaka dazuka, da kyautata muhallin halittu na filayen ciyayi, da ma nunawa duniya basira, da salon bunkasuwa na yankin Dalad ta fuskar shawo kan kwararar hamada.
A dai wannan babban birnin na Ordos, akwai wani yanki na kare muhalli mai daraja mai suna “Lotus Hills”, wanda ke can yankin Jungar. Yanki ne mai wurare masu ban sha’awa, da albarkatun karkashin kasa masu kima, musamman bangarorin haduwar kasa na Danxia, da ruwa mai kwarara da sauran su. Karamar hukumar wurin na aiki tukuru wajen ingiza bunkasar yawon bude ido a yankin, ta hanyar samar da karin ababen more rayuwa. A lokaci guda kuma, an gina karin abubuwa masu jan hankalin ‘yan yawon shakatawa, wanda hakan ke da matukar muhimmanci a fannin bunkasa yawon bude ido da raya al’adu.
Baya ga yankin “Lotus Hills”, manyan kwazazzaban Jungar da “Yellow River” ko Rawayar Kogi ya ratsa ta cikin su, na cikin manyan kwazazzabai 10 dake sassan kasar Sin. A wannan wuri Rawayar Kogi yana jujjuyawa, tare da samar da wani yanayi mai kayatarwar na daukar hotuna masu ban sha’awa. Akwai wata Babbar Ganuwa dake kafe a bakin kogin, ga kuma wuraren tarihi na zamanin da can barbaje a yankin, ciki har da dadadden kauyen Cui mai tarihin sama da shekaru 170, wanda ake zuwa kallon kayayyakin cikinsa masu tunawa jama’a yanayin rayuwar al’ummun da suka gabata. Baya ga kauyen Cui, akwai kuma gidan adana kayan tarihi na “Yellow River” wanda shi ma yake a sashen kwazazzaban Jungar. Gidan ya kunshi kayan fasahohi da ake iya zuwa kallo, da abubuwan al’adu, da shahararrun zane-zane masu nasaba da makwararar Rawayan Kogi. Ta hanyoyin watsa bayanai daban daban, an samar da damar yayata al’adun “Yellow River”, da al’adun makiyaya dake kewaye da shi, da al’adun Babbar Ganuwar wurin da sauran su. An kuma sake samar da hanyar dorewar tarihin dunkulewar al’adun Mongolia da na Han, tare da cimma nasarar bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummun wurin.
Bayan ziyartar wasu sassa na birnin Ordos sai kuma muka mika zuwa birnin Hothot, fadar mulkin jihar Mangolia ta gida, inda muka sauka a garin Laoniuwan wanda ya shahara da bishiyoyin dan itacen bakin kogi mai suna Haihongguo wanda ke kama da jar-dinya. Garin wanda ke a gundumar Qingshuihe karkashin birnin Hothot na jihar Mangolia ta gida, yana da nau’in kasa mai dacewa da tsiron na Haihongguo. A yankunan wannan gari an shuka sama da eka 1,000 ta nau’o’in Haihongguo, wanda hakan ya samar da yanayin dajin kare muhallin halittu mai kayatarwa. Kari kan hakan, a wannan gari an samar da tsarin hade ayyukan masana’antun shuka tsiron Haihongguo da bincike kansa, da kuma samar da ci gaba, baya ga harkokin raya al’adu da yawon bude ido da sauransu, wanda hakan ya haifar da wani yanayin gari na kare muhallin halittu mai matukar kyaun gani a yankin da garin yake.
A bangaren kare al’adun wannan yanki kuwa, mun ganewa idanun mu yadda aka kyautata cibiyar kauyen Gaomaoquan ta al’ummar Hohhot, wanda shi ne aikin farko da aka aiwatar a fannin raya al’adun yankin. A shekarar 2020 aka sake gina wani dadadden gida dake kauyen, tare da daga martabarsa zuwa cibiyar bincike mai daraja ta adana kayayyakin tarihin mazauna yankin, ta yadda aka hade al’adun gidaje, da wuraren cin abinci, da na nishadi, da sauran sassa wuri guda. Ta hanyar dogaro kan albarkatun yankin, da al’adun noman hatsi da sauran albarkatu, an kai ga bunkasa sashen binciken al’adun abinci da sauran ayyuka masu nasaba. A daya bangaren kuma dalibai da suka kammala karatu a kwalejoji dake komawa gida, da masu fasahohi daban daban mazauna yankin suna kara nuna sha’awar su ta shiga sana’o’in da ake rayawa a yankin. Kari kan hakan, cibiyar kauyen ta hade ayyukan shuka, da bunkasa albarkatun noma, da cin gajiyar albarkatun muhalli, zuwa aikin kyautata rayuwar kauye mai matukar inganci, da fadada samar da sassan kudaden shiga ga daukacin mazauna kauyen.
Birnin Hohhot, na jihar Mongolia ta gida ya shahara a matsayin “Cibiyar sarrafa madara”. A yankin kyautata lafiya na zamani na Yili, an kafa babban tsarin masana’anta da ya hade sassan samar da ci gaba mai kunshe da raya sana’ar shuka, da samar da madara, da amfani da na’urorin zamani wajen sarrafa hajojin ta, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasahohi, da raya sana’ar yawon shakatawa ta al’adu, da samar da nishadi, da gudanar da hada hadar kasuwanci. Baki dayan tsarin na da burin samar da salon sarrafa hajoji mafi inganci na zamani ta amfani da hanyoyi marasa gurbata muhalli, da kuma samar da ci gaban albarkatun abinci mai aiki da fasahohin kirkirarriyar basira ko AI.
Har ila yau, baya ga katafaren aikin samar da lantarki ta amfani da hasken rana na yankin Dalad dake birnin Ordos da na ambata a baya, a birnin Hothot ma akwai wani babban aikin samar da lantarki na kasa ta amfani da fasahohin zamani. Aikin ya na kunshe da tsarin hade wasu fasahohi na kirkire kirkire daban daban wuri guda.
Yayin samar da lantarki ta wannan salo ana yin tattalin kwal, da ruwa, da lantarki zuwa matsayi mafi kyau da ake iya cimmawa a matakin gida da ma kasa da kasa. Wannan tsari ya tabbatar da salon samar da makamashi abun dogaro kuma mai tsaro. A zango na biyu na samar da lantarki ta wannan fasaha, kamfanin Jinshan Thermal Power Company ya yi nasarar gina wata katafariyar hasumiyar sanyaya tururi mai tsayin mita 228.031, wadda ta zamo irin ta mafi tsayi a duniya baki daya. Wannan bajimta ta sanya a ranar 1 ga watan Disamban shekarar 2023 da ta gabata, kamfanin ya lashe lambar bajimta ta “Guinness Book of Records”.
Hukumar lura da makamashi ta jihar Mongolia ta gida ta jagoranci fadada wannan muhimmin aiki, wanda bayan kammalarsa, kamfanin na “Jinshan thermal power plant” zai rika samar da kimanin KWH biliyan 7.26 na lantarki a duk shekara, baya ga dumi da zai wadaci fadin wurin da zai kai kusan sakwaya mita miliyan 30. Kaza lika wannan muhimmin aiki ya kara samar da guraben ayyukan yi, da ingiza harkokin tattalin arziki da zamantakewar yankin gaba, kana hakan ya ba da damar cimma nasarar yakin da ake yi da gurbatar iska a ayyukan samar da makamashi.
Kafin karkare wannan ziyara, sai da muka ziyarci harabar katafaren kamfanin samar da hidimar aikewa da sakwanni na ZTO na kasar Sin. Kamfanin da ya bunkasa zuwa mai gudanar da hada hadar kasuwanci mafi girma a fannin sa, kana mafi masun ci gaba a jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kai. Cibiyar sa dake birnin Hothot tana amfani da na’urorin zamani irin su na farko a duk fadin kasar Sin wajen tsara rarraba kaya, wadanda ke iya aikin da ya kai kaso 90 bisa dari ba tare da sanya hannun mutum ba, wanda hakan ya sanya ta zama cibiya mai matsayin koli a fasahar rarraba kayayyaki mai amfani da nau’urori masu sarrafa kan su, kana mai na’urori dake iya ware kayayyaki mafi inganci a jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kai ta kasar Sin.
Alal hakika wannan ziyara ta kara bude idanu na game da ci gaban da sassan kasar Sin ke samu ta fannoni da dama, inda a wurare kadan cikin birane uku da muka ziyarta a jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kai dake arewacin kasar Sin, na ganewa idanu na yadda aka hade sassan ci gaba da dama, kama daga raya sha’anin noma da kiwo da sarrafa albarkatun su, da kyautata rayuwar mutane masu rauni da inganta kiwon lafiya, da raya kauyuka da sana’o’in hannu, da kare al’adun gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni, zuwa bunkasa sha’anin yawon bude ido, da samar da makamashi ta amfani da albarkatu da suka hada da iska, hasken rana, kwal da fasahar sarrafa tururi, da kare kwararar hamada da sauran su. Tabbas akwai tarin abubuwan koyi daga ci gaban kasar Sin, kuma muhimmai daga ciki su ne jagoranci na gari, da samar da tsare-tsare masu inganci da aiki tukuru, uwa uba kuma sanya moriyar jama’a gaban komai ta yadda za a gudu tare a tsira tare!