A duk fadin duniya a halin yanzu, kowa ya amince da cewa, fasahar kirkirarriyar basira ta AI ta taho da guguwar sauye-sauye da suka zama wajibi masu neman ci gaba ta ko wace fuska su runguma, wadanda suka tsaya sanya kuwa, za a bar su a baya suna tsintar hula.
Kasar Sin ta fahimci yadda fasahar AI ke da matukar alfanu wajen zamanantar da masana’antun da ake da su yanzu, da kuma ba da damar kafa sabbi. Rahoton ayyukan gwamnatin Sin na shekarar 2025 ya muhimmanta shirin “bunkasa tagomashin kirkirarriyar basira ta AI” bisa yadda kasar ta kudiri aniyar zage damtse wajen gwama fasahohin zamani da ayyukan masana’antu da kuma kasuwanci. Wannan ba kawai kasar Sin zai amfanar ba har da duniya, domin kasar ce ta fi ko wacce yawan masana’antu a duniya kuma babu wadda ta kamo ta a cikin shekaru 15 da suka gabata.
- Kasar Sin Za Ta Yi Ramuwar Gayya Kan Takunkumin Biza Da Amurka Ta Kakaba Wa Jami’anta
- Trump Na Son Yin Wa’adi Na Uku Na Shugabancin Amurka
Kasar ta kafa masana’antu na gwajin fasahar AI na kasa 421, kana da wasu masana’antu masu aiki da fasahar sadarwa ta 5G fiye da 4,000. Gwamnatin kasar ta kuma yi alkawarin tallafa wa duk wani yunkuri na amfani da fasahar AI ta gwaji a manyan masana’antu tare da kakkafa sabbin sassan cibiyoyin sarrafa kayayyakin aiki na zamani wadanda suka kunshi motocin sabbin makamashi masu aiki da fasaha, da wayoyin salula da kwamfutoci masu aiki da AI da kuma mutum-mutumi masu fasaha.
Sakamakon hobbasar da kasar ke yi a bangaren kere-kere da kirkire-kirkire tun daga kan doron kasa har zuwa sararin samaniya, ‘yan kasuwar ketare da suka halarci taron dandalin raya kasar Sin (CDF) a birnin Beijing, da taron shekara-shekara na dandalin Boao na Asiya (BFA) na 2025, dukkansu sun sha alawashin fadada zuba jarinsu ko kuma kiyaye abin da suka zuba.
Shugaban kamfanin Siemens, Roland Busch daga Jamus, da Shugaban kamfanin lantarki na Schneider Electric, Jean-Pascal Tricoire daga Faransa da kuma Shugaban Kamfanin AstraZeneca, Pascal Soriot daga Burtaniya, sun yi amannar kasar Sin tana da mafita a kan rudanin tattalin arziki na duniya bisa yadda ta zama katafariyar cibiyar manyan fasahohin zamani. Wannan ya sa ake da tabbacin, kwalliya za ta biya kudin sabulu bayan kammala aiwatar da cikakken shirin “bunkasa tagomashin kirkirarriyar basira ta AI” ba ga kasar Sin ba kawai har ma da sauran sassan duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp