A ci gaba da tattaunawar da jarumin Kannywood TALLE MAI FATA, a wannan makon za ku ji yadda ya yi bayani na jan hankali ga abokan sana’arsa ta fim, inda ya ce, ya kamata suma su rika yin fina-finai masu ma’ana da zai ciyar da al’adun Hausawa gaba, ta hanyar yin amfani da sanya sutura mai ma’ana ba kamar yadda wasu ke yi suna jawo musu magana ba domin kaucewa duk wani zargi da zaginsu da jama’a ke yi. Ga dai yadda karashen tattaunawar ta kasance da wakiliyarmu RABI’ATU SIDI BALARABE
Wanne irin kalubale ka taba fuskanta cikin masana’antar tun daga farkon farawarka kawo yanzu?
Ni gaskiya a cikin Kannywood ban samu kalubale ba, saboda duk wanda mu’amala za ta hada ni da shi dayan biyu ne, na ganka kana fim na ce wane zo mu yi fim, in na fuskanci ba za mu daidaita ba sai na kyale ka, kin san cikin ‘yan fim din ma akwai masu jiji da kai koda kuna tare da su kuma ‘yan fim din, za su rika ganin kamar ko sun fi ku wani abu, idan na fuskanci a yanayinka akwai hakan sai na hakura na nemi wanda za mu yi daidai, domin ni na dauki sana’ar da nake yi sana’a ta neman abinci. Saboda fim abu ne da duk lokuta ko na ce duk sakan kudinka ne ya ke tafiya. Ka hayar kayan aiki, ka hayi wurin da za a yi da sauransu, kana kokari ka gama, kin ga ba zai yu ka yi mu’amala da wanda zai kawo ma wata matsala ba, a cikin Kannywood kenan, ni ba wata matsala da nake samu ko na taba samu. A wajenta kuma in akwai abin da ya ke ci mun tuwo a kwarya to abu guda daya ne shi ne kuma nake kallonsa a babban kalubale, misali; na shiga kamar facebook na ga yadda ake zagin ‘yan fim ake musu kallon kafirai, ake musu kallon masu luwadi, da sauransu. To da yawan lokaci idan ki ka kula ban taba fitowa na ce Allah ya isa ko kuma don me ya sa ba, kamar yadda wasu ‘yan fim suke yi, wani lokaci na kan bar wa Allah ban taba yi ba Allah ya sani, to ka yi mun sharri ka ce ‘yan fim, ko ka zagi Kannywood zagin nan da ka yi wa masana’antar Kannywood duk mu ne, in ka ce ka zagi Kannywood ko ka ce ‘yan Kannywood Ka-za shi ne babban kalubalen da ni ya ke ci min tuwo a kwarya, wanda da yawan lokaci in na kalla sai dai kawai na ce Allah ya isa na bar wa Allah. Saboda ni harkar ta mun komai kuma ina cikinta dari bisa dari, idan kuma na sanka kana zagin Kannywood in Allah ya yarda za ka ga na daina mu’amala da kai ko waye, haka nake tafiyar da lamarina. Wannan dai shi ne kalubalen da zan iya cewa, wanda a mafi yawan lokaci ma sai na ce ni zan daina ma harkar kwata-kwata dalili shi ne; yadda nake bude facebook nake kallo, haka surukaina suke kallo, haka ‘ya’yana, ina da da wanda a yanzu ya iya karatu watakil nan gaba in na bashi damar fara social media zai ga ana cewa; sana’ar babanshi kaza-kaza da sauransu, shi ne tsayayyen kalubalen da nake fuskanta saboda ba ka yi wa komai jama’u, sai ki ga mutane suna yi wa dukka Kannywood Jama’u, kuma wallahi abin da ake a wajen Kannywood ya fi abin da ake mara kyau a Kannywood, abin da ake yi mara kyau mutanen da ba ‘yan Kannywood ba ma kwata-kwata suna da yawa. Saboda shi dan fim yana da wata kariya, yanzu kamar ni da yawan abu zan ji tsoron yi saboda ko ban ji tsoro don komai ba zan ji tsoron za a iya ganin fuskata a ce wane ne, kuma muna da doka mai karfi, duk wani sanannen fuska ma bai isa ya yi wani abin ba, ba komai ka ke fitowa fili ka yi ba, sabanin wanda za ki ga ya fito fili kowa, mutum zai iya fitowa ya yi abinsa ma ba a san shi ya yi ba.
Ta wacce hanya ka ke ganin za a magance irin wadancan matsalolin da suke afkuwa?
Hanya daya da za a magance irin wannan matsalolin shi ne; Mu ma mu rika inganta fina-finanmu mu san wadanne irin fina-finai za mu rika yi, kuma dole ko an ki ko an so yanzu duniya ta kai da dolen-dole sai mun fito mun tallata kanmu yadda idan abu ya danganci addininmu za mu iya fitowa mu kare shi ko ta karfin Social Media ne. Yanzu misali; Kwanaki akwai wani mawakin Kudancin kasar nan ya yi waka ya dora wakar akan shafinsa, wani ya hau kan masallaci da jallabiyya suna rawa suna waka, to idan da ba mu da karfi a Social Media da da muka fito mu kai kalubalantarsa ba da ba zai goge ba, hakan kuma izgilanci ne ga addininmu. Ya kamata mu rinka kokarin cusa addininmu muna kokarin ciyar da addininmu gaba ta dalilin haka za a ga da yawa mun yi nasarar janyo hankalinsu daga wani addinin su shigo namu. Da irin wannan tunanin nake ganin mu ma kanmu da gefanmu, da yawan lokaci ni ma kaina da sai nake tunanin sai mace ta sa kananan kaya ko ta yi meye kafin a sai fim, inda haka ne kin ga fim kamar Izzar So da ba zai karbu ba. Idan ki ka kalli Izzar so za ki ga abin addini da aka rika yi da sauransu, hakan kuma ya sa ya karbu, to in za mu gyara fina-finanmu mu ma in sha Allahu mutum ko ya fito zai yi zagin zai rasa hujjar yin zagin, amma wani lokacin mu muke kafa hujja har a ce ga abin da muka yi, Allah dai ya sa mu dace.
Wadanne irin nasarori ka samu game da fim?
Gaskiya Nasarorin suna da yawa, tun da kin ga ga gida, ga mota, aure da ‘ya’ya, an je Makkah, duk sanadiyyar fim. Wallahi ina zaune wani ya kira ni ya ce min ka je a yi maka ‘passport’, na ce ina da ‘Passport’ ya ce to ka kawo za ka tafi Saudiya, to yawanci duk irin wadannan nasarori ne wanda ba zan manta da su ba, ga aure ma har guda biyu, kin ga duk irin wadannan nasarori ne da na sassamu, nasarorin suna da yawa wallahi.
Ya za ka bambanta wa masu karatu bambancin da ke tsakanin fina-finan baya da na yanzu?
To ai fina-finan baya da na yanzu gabaki daya babu hadi, bari na baki karamin misali, kamar me kallon fim ne a bidiyo, da wanda kuma yanzu ya zo yana kallo a CD, da wanda kuma ya zo yana kallo a DBD, da wanda yanzu kuma ya zo yana kallo a Youtube, sai yana ‘connecting’ a Bluetooth dinshi da bluetooth din TB dinshi yana kallo. Ko kuma kamar ki ce Bluetooth ne da Dender, to haka abin ya ke kullum duniya ci gaba take yi. ‘Da’ fina-finan da muke amfani da su kafin mu zo na ji labari Wana yana fada mun, idan za a yi ‘scene’ goma, za a yi daya misali a nan wajen, za a yi daya a can waje misali sai an yi tafiyar minti goma, za a yi goma kuma a wajen da sai an tafi shi ma tafiyar minti goma, to in aka yi ‘scene’ 1 a nan, to akwai ‘scene’ 3 ba za a yi a nan ba sai a tafi can wani waje a yi ‘scene’ 2, sai a dawo nan a yi ‘scene’ 3, sai a tafi can gaba ma a yi ‘scene’ 5, to kuma suka dawo in za su yi ‘editing’ ba a ‘computer’ suke yi ba, wahala dai tayi yawa, in za su yi ‘recording sounds’ shi ma dai wahala ne, amma yanzu fina-finan da muke yi kamar kyamarorin da muke amfani da su duniya ta ci gaba, duk yadda ka dau wayarka ka shiga google za ka samu Camera sabuwa a duniya?, in kana da kudinka za ka saye ta a Ali Baba, ko kuma wani wajen sai da kayayyaki na duniya. Sannan za ka nemo ma’aikatanka wanda za su sarrafa ma duk kayan da ka ke so, za ka iya fita kowacce kasa ka yi ‘dauki fim, sabanin ‘da’ duk babu wannan, saboda haka fina-finan ‘da’ da na yanzu gaba daya ba bambanci, inda za a sami bambanci sai dai a ce labaran ‘da’ , zan ce e! akwai labarai masu ban sha’awa, ‘da’ ana fim na al’ada, na gargajiya yana bada sha’awa, yanzu kuma sai aka dawo ana ‘series’ fim a sa kananan kaya ana kwaikwayon turawa, wanda su fina-finan ‘da’ wanda ake kwaikwayon turawa za ki ga baya burge duniya, amma fina-finanmu na al’adarmu mu yi da kayan aiki na zamani za ki ga yana burge duniya. Kuma ko ‘international Award’ kake nema in ka saka ‘Jeens’ da T-shirt, macen ta saka wando da riga za ki ga fim din ba inda zai je, amma in ka dauko fina-finanmu muna da tarihi mu Hausawa, in aka dauko irin tarihin Hausawan nan fina-finan suna yin kyau sosai, bambancin kenan.
Mene ne burinka na gaba game da fim?
Na rika yin fina-finai wadanda za su janyo hankalin mutane daga aikata ayyuka marasa kyau su dawo suna aikata mai kyau, duk fim din da zan yi ya zama in sha Allahu akwai wani jan hankali, ko kuma fim din yana tafiya ne gaba daya akan jan hankalin mutane musamman matasa su daina yin abubuwa marasa kyau su dinga yin abubuwa masu kyau, ba ni da burin da ya wuce wannan don duk wani burina a harkar fim Alhamdulillahi na samu.