• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mugun Matakin Amurka A Tekun Kudancin Kasar Sin Ba Zai Yi Nasara Ba

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Nan da kusan wata guda, kasar Amurka ta aiwatar da mataki a tekun kudancin kasar Sin, na aika jiragen ruwan yaki zuwa kofar yankin kasar Sin don ta da hankali.

A waje guda kuma, ta yi wa kasar Sin batanci, wanda ya sa ta daukar matakin kariya na halal ala tilas, ta mayar da kasar a matsayin “mai zafin kai”.

  • Shugaban Kasar Sin Ya Nazarci Yanayin Tattalin Arzikin Tare Da Bitar Rahoton Ladabtarwa

A matsayinta na wata kasa dake nesa da shiyyar, Amurka ta nuna karfinta a kan tekun kudancin kasar karkashin tutar “’yancin zirga-zirga” na tsawon shekaru da dama, wanda shi ne babban dalilin da ya sa ake son inganta aikin soja a tekun kudancin kasar Sin.

A bayyane take, Amurka ta yi matukar keta hurumin kasar Sin da tsaronta, kuma ta yi mummunar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, amma ta sanya hular “mai zafin kai” da ta dinka saboda kanta a kan kasar Sin, wadda ke kiyaye mulkin kai da tsaron kasa, da nufin dora laifi kan Sin, da tsokanar dangantaka tsakanin Sin da makwabtanta wadanda dukkansu suke bakin tekun kudancin Sin, ta yadda za a tayar da rikici a yankin.

Shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 20 da rattaba hannu kan sanarwar matakan bangarori daban daban da suka shafi tekun kudancin kasar Sin.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 

Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC

A cikin shekarun 20 da suka gabata, dukkan bangarorin sun bi sanarwar a tsanake, tare da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, tare da kiyaye ‘yanci da tsaron zirga-zirga a yankin.

Yanzu, kasashen yankin sun kware da himma, da jagorancinsu, wajen magance faruwar hadaruka a yankin tekun kudancin kasar Sin.

Duk yadda Amurka ta yi taguwar ruwa a yankin, za ta zama kamar guguwar ruwa da ke tahowa, kuma ba za ta cimma nasara ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 
Daga Birnin Sin

Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 

October 30, 2025
Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC
Daga Birnin Sin

Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC

October 30, 2025
Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya

October 30, 2025
Next Post
Farashin Tikitin Jiragen Sama Ya Yi Tashin Gwauron-Zabi A Nijeriya 

Farashin Tikitin Jiragen Sama Ya Yi Tashin Gwauron-Zabi A Nijeriya 

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara

An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara

October 30, 2025
Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 

Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 

October 30, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara 

October 30, 2025
Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC

Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC

October 30, 2025
Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray

Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray

October 30, 2025
Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya

Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya

October 30, 2025
Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

October 30, 2025
Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

October 30, 2025
Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

October 30, 2025
Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

October 30, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.